Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-17 16:11:08    
Motoci da sabbin makamashi a kasar Sin

cri

A gun wasannin Olympic da aka kammala kwanan baya ba da jimawa ba a nan birnin Beijing, an kaddamar da sabbin motoci 595 da ake amfani da sabbin makamashi wadanda Sin ita kanta ta kirkiro da kuma kera, domin gudanar da hidimomi ga wasannin Olympic. Wadannan motoci sun yi amfani da sabbin makamashi, kuma ba su fitar da iska mai guba ba, sabo da haka, sun samu yabo sosai daga 'yan wasa da malaman wasa na kasashe daban daban.

Sa'an nan, a ran 11 ga watan Janairu na shekarar 2008 da muke ciki, wasu motocin fasinja 30 masu fasahohin zamani da kamfanin Foton na kasar Sin ya kera, wadanda ke amfani da sabbin makamashi tare da makamashin gargajiya sun fito a titunan birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin. Ya zuwa yanzu dai, wadannan motoci sun riga sun kama hanyoyin da tsawonsu ya kai kilomita sama da miliyan daya da dubu 200 ba tare da matsala ba. Motocin na cin mai da matsakaicinsa ya kai liter 30.5 a ko wadanne kilomita 100, wanda ya ragu fiye da kashi 25% bisa na motocin fasinja na gargajiya. Sa'an nan, hayaki mai guba da suke fitarwa ma ya ragu ainun.

Gwamnatin kasar Sin na kokarin bunkasa motocin da ke amfani da sabbin makamashi. A gun babban taron dandalin tattaunawa kan motoci masu amfani da sabbin makamashi na Sin a karo na farko da aka gudanar kwanan baya ba da dadewa ba, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin, Mr.Wan Gang ya bayyana cewa, ana sa ran bisa kokarin da bangarori daban daban ke yi, ya zuwa shekarar 2012, yawan motoci masu amfani da sabbin makamashi zai dau kashi 10% na motocin da Sin ke kera a duk shekara. Ya ce, "idan mun iya mallakar motoci masu amfani da sabbin makamashi da yawansu ya kai miliyan 1 a shekarar 2012, to, yawan man gasoline da za a rage yin amfani da shi zai kai liter miliyan 780 a duk shekara, haka kuma za a rage fitar da iskar Carbon Dioxide da yawansa ya kai ton miliyan 2 da dubu 300, wanda zai ba da babban taimako ga al'ummarmu a wajen rage amfani da makamashi da samun dauwamammen cigaba."


1 2 3