
'Dakin Tingliguan wani gine ne da aka gina bisa salon gine-gine na zamanin daular Qing na kasar Sin, kuma an yi masa ado a ciki bisa yadda salon fadar sarakuna. Mutane su kan ga bambanci in suka isa wurin. Akwai labaru da dama game da abincin da muke samarwa a nan. Mutane suna iya cin abinci da kuma kara fahimtarsu kan al'adun abinci.'
Domin maraba da gasar wasannin Olympic ta Beijing, an yi kwaskwarima kan wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, kazalika kuma, an ba da hidimomi daga dukkan fannoni a nan domin biyan bukatun baki daga kasashen waje. 1 2 3
|