Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-14 16:51:34    
Fadar shakatawa na sarakuna a yanayin zafi wato Summer Palace mai suna Yiheyuan a Beijing

cri

An yada fasahar zayyana lambuna ta kasar Sin sosai a wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, akwai ni'imtattun wurare masu ban mamaki da yawa a nan.

Wata doguwar rumfa tana kasancewa kudancin babban dutsen Wanshoushan a cikin fadar, tana fuskanta tabkin Kunminghu, tsawonta ya kai mita 728, ita ce doguwar rumfa ta gargajiya mafi tsayi a duniya. Mambobin sarakuna sun gina ta ne domin more idonsu da ni'imtattun wurare na fadar a yayin da ake ruwan sama ko kuma dusar kankara. A ko wane ginshikin rumfar an yi zane-zane, yawan zane-zanen ya wuce dubu 8, kuma suna shafar ni'imtattum wurare da furanni da tsuntsaye da kifaye da tsutsotsi da labaru game da mutane. Wannan rumfa tana daya daga cikin ni'imtattun wuraren da masu yawon shakatawa suka fi son ziyara, inda suke iya kallon ni'imtattun wurare, haka kuma, sun iya kara saninsu kan al'adun kasar Sin mai dogon tarihi bisa wadannan kyawawan zane-zane. Ewa, wata mutumiyar kasar Poland ta kawo wa kasar Sin ziyara sau da dama. A ko wane karon da ta yi bulaguro a wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, ta kan nuna babban yabo ga wannan rumfa. Ta ce,

'Wannan rumfa na da kyan gani sosai. Ban taba ganin irin wannan rumfa mai kyan gani kamar haka a sauran wurare na duniya ba, musamman ma bayan da aka yi mata kwaskwarima, ta kara kyan gani.'

Baya ga ni'mtattun wurare da wuraren tarihi masu tarin yawa, a cikin wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, akwai wani wuri da ya cancanci cin abinci irin na sarakuna, sunansa shi ne Tingliguan. A can da, sarakuna da matansu su kan saurari wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin da kuma gudanar da sauran harkokin nishadi a nan, amma bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, dakin Tingliguan ya zama wurin da aka karbi baki masu girma daga kasashen waje.

Ya zuwa yanzu, ana kiyaye dakin Tingilguan bisa salon gine-gine na gargajiya. Dukkan sabis suna sanya tufafi irin na gargajiya da aka taba sanyawa a fada. Mutanen da suka ci abinci a dakin Tingliguan su kan gane cewa, suna cin abinci a cikin dakin cin abinci na sarakuna. Sa'an nan kuma, ko wane abinci da ake samarwa a dakin Tingliguan yana da labarinsa, shi ya sa a lokacin cin abinci, sabis su kan yi wa mutane bayani kan wadannan labaru. Zhao Tongyi ya yi shekaru 30 ko fiye yana aiki a dakin Tingliguan, ya gaya mana cewa,


1 2 3