Kasar Sin ta yi suna ne saboda fasahar zayyana lambuna. Fadar shakatawa ta sarakuna a yanayin zafi wato Summer Palace da muke kiranta Yiheyuan da ke arewa maso yammacin Beijing, lambun sarakuna ne da aka yi mata cikakken adana a kasar Sin. Yana kasancewa wani dakin ajiye kayayyakin tarihi, kuma an gina shi ne bisa fitacciyar fasahar gine-gine da al'adu da kuma fasaha. Ba kawai fadar yanayin zafi ta shahara a gida ba, har matafiya masu yawa daga kasashen waje sun mayar da shi daya daga cikin wuraren da tilas ne su kai musu ziyara. Yau ma bari mu yi yawo a cikin wannan lambun sarakuna da aka fara ginawa a zamanin daular Qing ta kasar Sin, wato yau da shekaru 250 ko fiye da suka wuce.
A ran 2 ga watan Disamba na shekarar 1998, hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta nada wurin yawon shakatawa na Yiheyuan a matsayin wurin tarihi na al'adu na duniya. A ko wace shekara, mutane suna ta kawo wa fadar yanayin zafi ziyara daga gida da kuma waje. Madam Li Kun, wata jami'ar hukumar kula da wurin yawon shakatawa na Yiheyuan ta yi mana karin bayani cewa,
'A matsayinsa na abun ishara a tarihin lambuna na kasar Sin da kuma dukiyar al'adu ta duniya, fadar yanayin zafi ta kan karbi masu yawon shakatawa har da miliyan 1 a ko wace shekara, ciki yawan wadanda suka zo daga kasashen waje ya wuce kashi 15 cikin dari. Fadar yanayin zafi ta nuna muhimmanci sosai wajen nuna kyakkyawar surar Beijing da kuma yin mu'amala tare da kasashen waje.'
Akwai ni'imtattun wurare da yawa a cikin fadar, sa'an nan kuma, wannan wurin yawon shakatawa yana matsayin dakin ajiye kayayyakin tarihi da na al'adu. A shekarun baya, an yi kwaskwarima kan muhimman ni'imtattun wurare a matakai daban daban a fadar, ta haka wannan wurin yawon shakatawa mai dogon tarihi ya sake nuna kyan ganinsa. Madam Li ta gaya mana cewa,
'A matsayinsa na wurin tarihi na al'adu na duniya, a ko wace shekara hukumarmu da gwamnatin kasar Sin sun zuba makudan kudade tare da aikawa da kwararru da yawa kan kiyaye wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, domin tabbatar da ganin zai sami ci gaba mai dorewa, haka kuma, zai nuna kyan ganinsa a matsayin lambun sarakuna kamar yadda yake zama a farkon kafuwarsa wato yau da shekaru 250 ko fiye da suka wuce.'
1 2 3
|