Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-13 16:27:19    
Makomar tattalin arzikin kasar Sin bayan bala'in girgizar kasa

cri

Kamar yadda aka yi nazari a cikin wannan rahoto, lokacin da ake sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa, tabbas ne farashin kayayyakin makamashin halittu da na masarufi zai karu. Sakamakon haka, kasar Sin za ta fuskanci wata matsalar da ke tsone wa mutane ido lokacin da take tsara manufofin tattalin arziki bisa dukkan fannoni, wato ana bukatar kara ba da rancen kudi domin sake raya yankuna masu fama da bala'in, amma a waje daya, idan farashin ma'adinai da albashin 'yan kwadago su karu, mai yiyuwa ne za a kara samun raguwar darajar kudi.

Game da wannan matsala, Mr. Ji Ming, direktan ofishin yin nazarin tattalin arziki daga dukkan fannoni na bankin jama'ar kasar Sin ya ce, ya kamata a ci gaba da aiwatar da manufar tsuke bakin aljihu game da harkokin kudi.

"Muhimmin nauyin da ke bisa wuyanmu wajen sa ido kan tattalin arziki daga dukkan fannoni shi ne a ci gaba da yin rigakafin aukuwar matsalar raguwar darajar kudi. Sabo da haka, ya kamata mu ci gaba da aiwatar da manufar tsuke bakin aljihu game da harkokin kudi."

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, bayan aukuwar bala'in girgizar kasa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta riga ta kebe biliyoyin kudade domin aikin ceto, kuma ta kafa wata asusun sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa. Wadannan kudade za su taka rawa wajen sa kaimi kan mutane da su kashe kudi kan kayayyakin masarufi, da kuma su zuba jari. Sakamakon haka, za a iya kara saurin raya masana'antu da zuba jari a karshen rabin shekarar da muke ciki.


1 2 3