Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-13 16:27:19    
Makomar tattalin arzikin kasar Sin bayan bala'in girgizar kasa

cri
 

Haka kuma, wannan jami'i ya ce, jarin da ake zubawa da kayayyakin da ake fici da kudaden da ake kashewa su ne muhimman abubuwa ukku da ke ciyar da tattalin arzikin kasar Sin gaba. Bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan bai yi mummunar tasiri ga wadannan abubuwa ukku ba. Sabo da haka, bala'in girgizar kasa ba zai yi mummunar tasiri ga ainihin halin da kasar Sin ke ciki a fannin tattalin ariki daga dukkan fannoni. A ganin Mr. Yi Xianrong wanda ke nazarin sha'anin kudi a cibiyar nazarin ilmin zaman al'umma ta kasar Sin yana ganin cewa, tare da kudade mai yawan gaske da gwamnatin tsakiya ta zuba, tabbas ne za a maido da zirga-zirga da ayyukan jama'a na birane da gidajen kwana na wadannan yankuna ta yadda za su koma halin da ake ciki kafin aukuwar bala'in girgizar kasa. Wadannan kudaden da ake zubawa za su zama wani muhimmin karfin karuwar GDP na kasar Sin. Mr. Yi ya ce, "Lokacin da ake sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa, za a zuba kudade mai yawan gaske. Tabbas ne wadannan kudade za su zama karfin ciyar da tattalin arzikin wadannan yankuna gaba cikin sauri. A waje daya kuma, a lokacin da ake sake raya wadannan yankuna, tabbas ne za a ciyar da sana'o'i da masana'antun da abin ya shafa gaba. An kiyasta cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai karu da kashi 2 ko kashi 3 cikin kashi dari sakamakon aikin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa."

Bugu da kari kuma, baki 'yan kasuwa da ke lardin Sichuan ba su rasa imaninsu kan cigaba da zuba jarinsu a lardin Sichuan. Bisa binciken da kwamitin sa kaimi kan zuba jari na birnin Chengdu, hedkwatar lardin Sichuan ya yi a masana'antu masu jarin waje fiye da dubu 1, an bayyana cewa, bayan kwanaki 10 da aka samu bala'in girgizar kasa, masana'antun da yawansu ya kai kashi 80 cikin kashi dari sun farfado da aikinsu. A cikin manyan kamfanoni 130 wadanda suke cikin kamfanoni 500 mafi girma a duniya, kuma suke da masana'antunsu a birnin Chengdu, yawancinsu sun riga sun farfado da aikinsu. Lokacin da wakilinmu yake ganawa da baki 'yan kasuwa da ke birnin Chengdu, ya gane cewa, har yanzu baki 'yan kasuwa suna da imani ga shirinsu na zuba jari a lardin Sichuan. Mr. William Gan Kian Hock, babban direktan masana'antar kamfanin NCSI, wato wani kamfanin kimiyya da fasahar na'urorin sadarwa na kasar Singapore da ke birnin Chengdu ya ce, "Muna kokarin gaya wa bakinmu da hedkwatarmu da ke ketare cewa, ba a samu lalacewa ba a birnin Chengdu. An riga an komar da odar zaman rayuwar yau da kullum. Musamman ba a yi mummunar tasiri ga tsarin samar da ruwan sha da wutar lantarki da na yanar gizo da na sadarwa da kuma filin jirgin sama ba. Sabo da haka, ba za a kawo illa ga bunkasuwar masana'antarmu ba."

Haka kuma, Mr. Afred Ling, mataimakin babban direktan zartaswa na kamfanin sadarwa na Ericsson da ke nan kasar Sin ya kuma bayyana cewa, yana cike da imani ga makomar kamfaninsu.

"Ba a samu sauye-sauye sosai ba a birnin Chengdu. Ana tafiyar da tattalin arziki kamar yadda ya kamata. 'Yan kwadago ma suna da karfin yin takara kamar da. Haka ne an samu bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan, amma ina tsammani cewa, aikin sake raya wadannan yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa zai kawo mana damar neman bunkasuwa da yawa."

Bugu da kari kuma, lardin Sichuan ba muhimmin sansani ne na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ba, ba zai yi babban tasiri ga cinikin waje na kasar Sin ba. Cibiyar nazarin sha'anin kudi ta bankin tsakiya na kasar Sin ta yi tsammani cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da girma sosai. Bukatun da ake nema a cikin gidan kasar Sin za su bayar da muhimmiyar gudummowa ga cigaban tattalin arzikin kasar Sin. Idan aka rage saurin cinikin waje, ba za a kawo illa ga cigaban tattalin arzikin kasar Sin ba.

Kazalika kuma, a fannin saya da sayarwa, yanzu ana samar da isassun kayayyaki a kasuwar kasar Sin, kuma ana da karfi sosai wajen saya da sayarwa. Sabo da haka, aikin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa zai sa kaimi ga cigaban kasuwar cinikin kayayyakin gini ta kasar Sin. A cikin wani rahoton da cibiyar nazarin sha'anin kudi ta bankin jama'ar kasar Sin, wato bankin tsakiya na kasar Sin ta bayar a kwanan baya, an ce, za a kara zuba jari a masana'antun samar da kadarori lokacin da ake tafiyar da shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in, sannan kuma yawan abinci da sauran kayayyakin masarufi da ake nema bayan bala'in zai karu.


1 2 3