Bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan a ran 12 ga watan Mayu ya haddasa babbar hasara ga larduna da dama. A waje daya kuma, wannan bala'in girgizar kasa ya sanya mutane sun mai da hankulansu kan makomar tattalin arzikin kasar Sin. Sabo da haka, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani bayani game da tasirin da wannan bala'in girgizar kasa ya kawo wa kasar Sin da makomar tattalin arzikin kasar Sin bayan wannan bala'in.
A ran 12 ga watan Mayu na shekara ta 2008, an samu bala'in girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Wannan bala'in girgizar kasa ne da ya fi shafar yankuna mafi yawa tun daga shekarar 1949. Ba ma kawai ya kawo illa ga lardin Sichuan ba, har ma ya kawo illa sosai ga lardunan Shaanxi da Gansu da Chongqing da Yunnan da Guizhou. Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka mutu a cikin wannan bala'in girgizar kasa ya riga ya kai kusan dubu 70. Jimlar hasarar tattalin arziki da wannan bala'in girgizar kasa ya haddasa kai tsaye ya kai kudin Sin yuan biliyan 845.1, daga cikinsu, yawan hasarar tattalin arziki ta lardin Sichuan ya kai kashi 91 cikin kashi dari.
Bisa kididdigar da kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin da bankin jama'ar kasar Sin suka yi, an ce, ko da yake bala'in girgizar kasa na Wenchuan ya haddasa hasarar tattalin arziki mai tsanani a yankuna masu fama da bala'in, kuma ya kawo illa sosai ga aikin kawo albarka da odar zaman rayuwa na wadannan yankuna, amma sabo da galibin yankuna masu fama da bala'in su yankuna ne na tsaunuka. Yawan tattalin arziki na wadannan yankuna ya yi kadan a cikin jimlar tattalin arzikin duk kasar Sin. Sabo da haka, wannan bala'in girgizar kasa ba zai canja ainihin halin da kasar Sin ke ciki a fannin tattalin arziki ba.
Mr. Mu Hong, mataimakin shugaban kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya bayyana cewa, an samu babbar hasara sosai a cikin wannan bala'in girgizar kasa, amma ya yi mummunar tasiri kadan ga jimlar kudaden samar da kayayyaki ta kasar Sin, wato GDP ta shekarar da muke ciki. Mr. Mu ya ce, "Yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa suna arewacin lardin Sichuan. Muna da imani cewa, bala'in zai kawo babbar illa ga lardin Sichuan gaba daya. Amma sabo da yawan GDP na lardin Sichuan ya kai kimanin kashi 4 cikin kashi dari kawai bisa jimlar GDP ta duk kasar Sin, yawan GDP na wadannan yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa sosai ya kai kashi kadan daga cikin kashi dubu. Sakamakon haka, tabbas ne muna ganin cewa, wannan bala'in girgizar kasa zai kawo illa ga jimlar GDP ta kasar Sin, amma irin wannan tasiri ya yi kadan."
1 2 3
|