Game da haka, shugaban hukumar nazarin sha'anin ba da ilmi ta kasar Sin Mr. Gu Mingyuan ya bayyana cewa,
'A cikin gajeren lokaci wato a cikin shekaru 30 da suka gabata, kasar Sin ta zama wata babbar kasa da ke da albarkar kwararru, amma a da kasar Sin ta yi baya a fannonin al'adu. Kasar Sin ta cim ma tudun dafawa a muhimman fannoni biyu, na farko, ta cim ma burin ba da ilmin tilas na shekaru 9, na biyu, ta cim ma burin shigar da yawancin jama'a cikin jami'o'i. Muna iya cewa, wannan ya zama abin al'ajabi ne.'
1 2 3 4
|