Mataimakin darektan hukumar da ke kula da dalibai ta ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin Mr. Jiang Gang ya gaya mana cewa,
'Tun daga shekarar 1999, kasar Sin ta fara gudanar da manufar kara shigar da 'yan makaranta zuwa jami'o'i, domin kara biyan bukatar al'umma a fannoin kwararru da suke da ilmi, da kuma biyan bukatar jama'a wajen karatu a jami'o'i. A cikin shekaru 10 da suka gabata wato daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2008, an shigar da 'yan makaranta miliyan 40 da dubu 100, yawansu ya kai kashi 75 cikin dari na dukkan dalibai da aka shigar da su zuwa jami'o'i a cikin shekaru 30 da suka gabata.'(Danladi) 1 2 3 4
|