Yanzu Sin da Afirka na ciniki ne cikin daidaici. A farkon rabin shekarar da muke ciki, yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 23, a yayin da yawan kayayyakin da Sin ta shigo da su daga kasashen ya kai dalar Amurka biliyan 30 da miliyan 100. Mr.Wang Shouwen, shugaban sashen kula da cinikin waje na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ya bayyana cewa, kasuwannin kasar Sin sun kara samar da zarafi ga Afirka, ya ce,"Bisa kididdigar da muka yi, tun daga shekarar 2000 har zuwa ta 2005, yawan kayayyakin da Sin ke shigowa da su daga Afirka na karuwa da kashi 30% a kowace shekara, a yayin da yawan kayayyakin da Afirka ke fitarwa zuwa kasashen duniya baki daya na karuwa da kashi 15% ne kawai a kowace shekara, wannan ya shaida cewa, kasuwannin Sin na kara samar da zarafi ga Afirka a maimakon barazana."
Akasarin kasashen Afirka na son Sin ta kara zuba musu jari, ta taimaka wajen kyautata tsarin masana'antunsu, kuma ta horar musu da kwararru, don kyautata karfinsu wajen samun cigaba. Ado Leko, konsula a ofishin jakadancin Nijer da ke Sin, ya ce,"hadin gwiwar ciniki na gudana yadda ya kamata tsakanin Sin da Afirka, idan mun ci gaba da hadin gwiwar, to, abin zai amfana wa bangarorin biyu baki daya. Ina ganin hadin gwiwar yana da kyau, kuma ina fatan zai ci gaba da gudana."(Lubabatu) 1 2 3
|