A ran 9 ga wata, jami'an ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin sun bayyana a nan birnin Beijing cewa, bisa taimakon da aka samu daga wajen taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka, hadin gwiwar ciniki da ke tsakanin Sin da Afirka ta bunkasa cikin sauri. Sin da Afirka na gudanar da hadin gwiwar ciniki ne bisa tushen girmama wa juna mulkin kai da kuma zaman daidaici da cin moriyar juna, hadin gwiwar ciniki da ke tsakanin Sin da Afirka na taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikinsu da kuma kyautata zaman rayuwar jama'arsu, wanda ya sha bamban sosai da mulkin mallaka.
An ce, tun bayan da aka fara gudanar da taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka a shekarar 2000, huldar ciniki da ke tsakanin Sin da Afirka sai dinga bunkasa take yi cikin sauri. Ya zuwa shekarar 2007, yawan cinikin da aka yi tsakanin Sin da Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 73 da miliyan 300, wanda har wa yau ke tabbatar da karuwa sama da kashi 30% a kowace shekara. Bisa kididdigar da asusun ba da lamuni na duniya ya yi, an ce, Sin ta riga ta zo ta biyu a wajen yin ciniki da Afirka.
1 2 3
|