Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-06 19:21:40    
Birnin Beijing ya kaddamar da sabbin matakan shawo kan cinkoson hanya domin kyautata ingancin iska da halayen zirga-zirga

cri

Mr. Du Shaozhong?mataimakin shugaban hukumar kiyaye muhalli ta birnin Beijing ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka tsai da sabbin matakan shawo kan cinkoson hanya shi ne, ban da ci gaba da kyautata halayen sadarwa, kuma wani muhimmin makasudi na daban shi ne domin kiyaye ingancin iska mai kyau na Beijing. Ya ce, "Bayan wasannin Olimpic na Beijing, duk zaman al'umma musamman ma tarin mutane 'yan birnin suna fatan ganin ranakun da za a samun yanayi mai kyau ya ci gaba da karuwa ba fashi. Domin ci gaba da kyautata muhallin birnin Beijing, musamma ma ga ingancin iska, da kiyaye sakamakon da aka samu, da kuma kafa tsari ba da amfani har lokaci mai tsawo wajen kyautata ingancin iska, shi ya sa muka tsai da matakan da abin ya shafa."

Wani saurayi mai sunan Deng Xitao wanda kuma wani ma'aikacin kamfani ne na birnin Beijing, a da yakan tuka mota a kowace rana domin zuwan wurin aiki da komawa gida, amma a lokacin wasannin Olimpic, sabo da matakan shawo kan cinkoson hanya da aka tsayar, shi ya sa an hana shi tuka mota cikin rabin yawan kwanaki. Ko da yake an kuntata masa wajen tafiyarsa, amma ya ce, "A lokacin wasannin Olimpic na Beijing, sabo da an kayyade yawan motocin da suke tafiya kan hanya, shi ya sa mutane fararen hula suka samu wahala kadan wajen zirga zirgarsu, amma ingancin iska ya kyautatu sosai bisa na da. Yanzu an kaddamar da sabbin manufofin sadarwa, dukkun mutane suna nuna musu goyon baya. Domin kyautata ingancin iska da kiyaye muhalli, daina tuka mota kwana daya a mako ba wani abu ba ne."


1 2 3