Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-06 19:21:40    
Birnin Beijing ya kaddamar da sabbin matakan shawo kan cinkoson hanya domin kyautata ingancin iska da halayen zirga-zirga

cri

A lokacin wasannin Olimpic da wasannin Olimpic na nakasassu na Beijing, birnin Beijing ya dauki matakan shawo kan cinkoson hanya wato ya gudanar da tsarin zirga-zirgar motoci masu lambobin mara da masu lambobin cika a ranakunsu, da haka ne aka kyautata ingancin iska da hana cinkoson ababan hawa. Dimin inganta wannan sakamakon da aka samu, da kafa tsarin kyautata ingancin iska da halayen sadarwa har zuwa lokaci mai tsawo, kwanan baya birnin Beijing ya kuma kaddamar da sabbin matakan shawo kan cinkoson hanya ta yadda za a rage mugun tasirin da aka janyo wa ingancin iska sakamakon gurbatacciyar iskar da ake fitarwa daga motoci, da samun tabbaci ga zirga-zirgar motoci.

Bisa sabbin matakan shawo kan cinkoson hanya da aka tsayar an ce, daga ran 1 ga watan Oktoba, da farko an hana tafiyar motocin da yawansu ya kai kashi 30 bisa 100 na hukumomin jam'iyya da na gwamnati bisa matakai daban na birnin Beijing, daga baya kuma za a hana tafiyarsu kwana daya a kowane mako bisa lambar karshe ta lambobinsu. Daga ran 11 ga watan Oktoba kuma cikin rabin shekara mai zuwa, za a aiwatar da matakan hana tafiyar motocin jama'a na birnin kwana daya a kowane mako bisa lambar karshe ta lambobinsu.


1 2 3