Da misalin karfe 9 ne, musulmi suka fara jam'i a karkashin jagorancin limamai. Bayan da aka kammala jam'i, masallacin ya shirya 'ya'yan itatuwa da sauran abinci, ya rarraba wa kowa. Sa'an nan, kowa ya koma gida. A nan kasar Sin, bayan da aka tashi daga masallaci, a kan kai wa juna ziyara, domin mika gaishe-gaishe na murnar sallah, a ci abinci tare, sa'an nan, a kan kuma je kaburburan iyalan wadanda suka rasu, domin tunawa da su.
Karamar sallah muhimmin biki ne ga musulmin duniya, musulmin kasar Sin su ma sun mika gaishe-gaishensu ga musulmi na kasashe daban daban. Da farko dai, bari malam Wang Chong'en, liman da ke masallacin Fayuan ya mika gaishe-gaishensa.
"Yau bikin karamar sallah ne ga musulmin duniya, sabo da haka, ina taya musulmin duniya baki daya murnar sallah."
Sauran musulmin kasar Sin ma suna son mika gaishe-gaishensu. 1 2 3
|