Ban da wannan kuma, aikata alheri a watan Azumi shi ma daya ne daga cikin muhimman abubuwan da musulmin kasar Sin ke yi a watan Ramadan. Mr.Liu Yushan, wani musulmi ne da ke zaune a nan birnin Beijing. ya ce:
"mu musulmi muna kira watan azumi watan Ramadan karim, wato wata mai girma ke nan. Sabo da haka, a watan azumi, abin da ya fi muhimmanci a gare mu shi ne mu aikata alheri, misali mu ba da taimako ga matalauta, mu lura da marayu da dai sauransu, wato mu aikata alheri bisa ga yadda aka jagoranta, mu ba da taimakonmu a wajen jin dadin al'umma."
Masu sauraro, ran 2 ga watan nan da muke ciki, musulmin kasar Sin sun kammala azumin watan Ramadan, kuma sun fara shagulgulan karamar sallah. A ran nan da safe, musulmin da ke zaune a kusa da masallacin Fayuan sun yi ta taruwa a masallacin, suna cikin farin ciki da walwala. Madam Ma Yingjie, wadda ke da shekaru 78 da haihuwa, tana cike da farin ciki, ta ce, watan azumi ya wuce, musulmi ko tsofaffi ko yara kanana, dukansu sun je masallaci domin jam'i, wannan rana ce ta farin ciki, musamman ma a shekarar da muke ciki, karamar sallah na da ma'ana ta musamman, ta ce:
"A kasarmu ta Sin, aka kammala wasannin Olympic ba da jimawa ba, mun cimma nasarar gudanar da wasannin Olympic, haka kuma mun cimma nasarar gudanar da wasannin Olympic na nakasassu, ga shi kuma yanzu mun fara murnar ranar kasar Sin da karamar sallah, dukan wadannan abubuwan farin ciki sun taru a gu daya ke nan, sabo da haka, yanzu muna cikin farin ciki a kowace rana."
A masallacin, mun kuma gamu da wasu shugabannin unguwar Xicheng ta birnin Beijing, wadanda suka je masallaci musamman domin taya musulmi murnar sallah. Masu sauraro, ba da 'yancin bin addinin da aka ga dama manufa ce da har kullum gwamnatin kasar Sin ke bi. Domin nuna girmamawa ga mabiya addinai daban daban, baya ga mika musu gaishe-gaishe a lokacin bukukuwan addini, gwamnatin kasar Sin tana kuma kokarin taimaka wa bangaren addini a wajen gudanar da harkokin addini daban daban. A lokacin karamar sallah ta wannan shekara, hukumomin gwamnati su ma suna kokarin samar da sauki ga musulmin kasar Sin. Mr.Chen Guang, mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin kabilu da addinai na hukumar unguwar Xicheng ta birnin Beijing ya ce:
"yau shugabannin sassan da abin ya shafa na unguwarmu, ciki har da sashen tsaro da wasu sassan ba da tabbaci wajen samar da ruwa da lantarki da dai sauransu, dukansu suna kokarin ba da taimakonsu, don taimakawa bangaren addini a wajen gudanar da harkokinsu yadda ya kamata, ta yadda mabiya addinin musulunci za su iya jin dadin bikinsu."
Domin tabbatar da 'yancin addini ga jama'a, gwamnatin kasar Sin ta kuma zuba makudan kudade a wajen horar da masu aikin addini da kuma bunkasa wuraren ibada. Yanzu a nan kasar Sin, akwai masallatai kimanin dubu 30, tare kuma da limamai fiye da dubu 40, wadanda ke daukar nauyin kulawa da musulmin kasar da kuma musulmin ketare da ke zaune ko kuma yawon shakatawa a kasar. Masallacin Fayuan wani tsohon masallaci ne da ke da tsawon tarihi na daruruwan shekaru. Amma da ma ya lalace sabo da ya dade, a shekarar 2003, gwamnatin kasar Sin ta zuba kudade ta gyara shi. Bayan da aka gyara shi, an fadada shi sosai da sosai, kuma an kara kayatar da masallacin a fannoni daban daban. A lokacin wasannin Olympic na Beijing, masallacin ya kuma dauki nauyin kulawa da 'yan wasa da masu yawon shakatawa na kasashe daban daban. Mr.Shareef, wani musulmin da ya zo daga Amurka, yana zaune a birnin Beijing a halin yanzu. A lokacin karamar sallah, shi ma ya zo masallacin Fayuan, ya ce:
"Wannan masallaci ne mai kyau, jama'a na da zumunci, kowace rana ina zuwa domin sallah, musulmin da ke nan suna da aminci."
1 2 3
|