Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-03 17:44:48    
Musulmin kasar Sin a watan azumi

cri

Ga shi yanzu watan azumi ya shige, kuma kwanan baya, bi da bi ne musulmai na kasashe daban daban suka fara shagulgulan murnar karamar sallah. A yayin da suke murnar sallah kuma, sun kuma aiko mana sakonninsu na taya murnar sallah, Muntaka Abdul Hadi Dabo daga Anguwar Fatika Zaria, ya ce, "na rubuto wannan wasika tawa ne don in taya al'ummar musulmi murnar karamar sallah da kuma kammala azumin watan ramadan. da fatan ubangiji ya karbi ibadunmu da kuma ayyukanmu. Allah ya maimaita mana na badin badada. A ci gaba da shagulgulan sallah lafiya." Sa'an nan kuma, masu sauraronmu da yawa sun nuna sha'awarsu game da zaman rayuwar musulmin kasar Sin a watan Ramadan da kuma yadda suke karamar sallah. Misali, Salisu Muhammed Dawanau daga Abuja, Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "shin yaya musulmin kasar Sin ke nasu azumin watan Ramadan?", ga kuma malama Fatima Muhammed daga Kano, Nijeriya, ta tambaya, "bayan azumin watan Ramadan ya shige, musulmin kasashe daban daban za su fara shagulgulan karamar sallah, shin yaya musulmin kasar Sin ke yi don murnar sallah?"

To, domin amsa tambayoyin masu sauraro, mun kai ziyara ta musamman ga masallaci mai suna Fayuan da ke nan birnin Beijing, don binciko muku yadda musulmin kasar Sin ke zaman rayuwa a watan azumi.

Masu sauraro, kasar Sin kasa ce da ke da mabiya addinai iri iri, kuma muhimman addinai da ake bi a nan kasar sun hada da Buddahism da Taoism da Musulunci da Kiristanci da kuma Katolika. Daga cikinsu kuma, musulunci ya shigo kasar Sin ne a wajen karni na 7, kuma yanzu 'yan kananan kabilu 10, ciki har da 'yan kabilar Hui da ta Uygur, suna binsa. Musulmin kasar Sin na zama kusan ko ina a kasar Sin, amma an fi samunsu ne a lardunan Xinjiang da Ningxia da Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Kamar yadda musulmin sauran kasashen duniya ke yi, musulmin kasar Sin su ma suna azumi a cikin watan Ramadan. Malam Wang Chong'en, wani limami a cikin masallacin Fayuan da muka ziyarta, ya bayyana cewa:

"A magariba, za mu yi sallah, sa'an nan a dare, za mu je masallaci mu yi jam'i. Bayan da muka koma gida, za mu dan huta kadan, sa'an nan, za mu karanta alkur'ani da kuma haddis. Daga bisani kuma, za mu shirya abinci mu ci abinci. Misali a yau, tun daga karfe 4 da rabi na alfijir, ba za mu ci abinci ba har zuwa karfe shida da minti 2 da maraice."


1 2 3