Jama'a, kamar yadda kuka san cewa, yawan mutanen kasashe masu tasowa ya dauki kashi 4 cikin kashi 5 na jimlar mutanen duk duniya. A idon Mista Wen, wanda shi ne firaministan wata kasa mai tasowa da ta fi girma a duniya, ma'anar makasudin bunaksuwa na shekarar 2000 ita ce , yin watsi da bambanci da tsallake shinge da kuma shimfida zaman jituwa na gaskiya a duniya. Yana mai cewa:
" Daga cikin zuciyata ne nake fatan wata rana talakawa za su ishi kansu wajen samun isasshen abinci da sutura, kuma dukan yara kanana za su samun damar shiga makaranta yayin da kowa da kowa yake samun kyakkyawan sharadin jinya da zaman alheri". ( Sani Wang ) 1 2 3
|