Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-26 13:43:13    
Halartar Wen Jiabao a babban taron MDD na shekarar 2000, wato MDGs

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, firaministan kasar Sin Mista Wen Jiabao ya halarci babban taron MDD na makaksudin bunkasuwa na shekarar 2000, wato MDGs da aka gudanar jiya Alhamis, agogon wurin, a birnin New York, babbar hadkwatar majalisar, inda ya fito da wasu jerin sabbin matakai da kasar Sin za ta dauka na tallafa wa kasashen ketare; Kana ya bayyana yadda gwamatin kasar Sin take aiwatar da makasudin bunkasuwa na shekarar 2000 na MDD, da halin hadin gwiwa da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa; Kazalika, ya gabatar da wasu shawarwari kan yadda kasashe daban-daban na duniya za su kawar da wahalhalun da suke sha wajen samun bunkasuwa da kuma aiwatar da makasudin bunkasuwa na shekarar 2000 daga dukkan fannoni.

Sanin kowa ne cewa, shirin " makasudin bunkasuwa na shekarar 2000" ya samu amincewa ne daga dukkan kasashe mambobin MDD a shekarar 2000. Babbar manufarta ita ce, kafin karatowar shekarar 2015 a rage yawan talakawa da rabi da aka taba samunsu a shekarar 1999. Wakilai daga kasashe sama da 150 sun halarci taron ciki har da shugabanin kasashe da na gwamnatoci sama da 90, inda babban sakataren MDD, Ban Ki-moon ya yi kira ga kasashe daban na duniya da su fuskanci kalubale iri daban-daban dake gabansu. Yana mai cewa: " A yanzu haka dai, muna wa gaba kan hanyar gaskiya. Ya kamata mu gaggauta daukar matakai don fuskantar kalubale iri daban-daban dake gabanmu don sanya babban karfi ga yunkurin tabbatar da makasudin bunkasuwa a fadin duk duniya".


1 2 3