Bayan da shugaban kungiyar tarayyar Afrika wato AU Mista Jakaya Kikwete da firaministan kasar Burtaniya Mista Gordon Brown suka yi jawabi, sai firaminista Wen Jiabao ya hau kan dakalin lacca na babbar hadkwatar MDD, inda ya yi gajeren bayani kan nasarorin da kasar Sin ta samu wajen rage talauci. Ya ce,cikin shekaru 30 da suka gabata, kasar Sin ta rage talakawa da yawansu ya wuce miliyan 230; Ban da wannan kuma, ta rage basussuka da yawansu ya kai kudin Sin wato RMB yuan billiyan 20 da miliyan 470 da take bin kasashe 49 mafiya talauci, wadanda kuma suke cin basussuka masu yawan gaske. Mr. Wen ya furta cewa: " A matsayin wata babbar kasa mai tasowa dake sauke nauyin dake bisa wuyanta, ko da yake kasar Sin ba mai hannu da shuni ba ce, amma ta rigaya ta cika alkawarin da ta dauka game da " Sanarwar shekarar 2000", wato ke nan ta bada taimako gwagwadon iyawa ga wassu kasashen da suka fi samun talauci a duniya".
Bugu da kari, Mista Wen Jiabao ya furta cewa, domin ingiza yunkurin tabbatar da makasudin bunkasuwa na shekarar 2000, gwamnatin kasar Sin za ta dauki wassu jerin sabbin matakai na tallafawa kasashen ketare. Wadannan matakai sun hada da cire rancen kudi da kasar Sin take bin kasashen da suka fi samun talauci, wadanda suka gaza biya mata kafin karshen shekarar da muke ciki; da nuna musu gatanci wajen biyan kudin kwastan na kashi 95 daga cikin 100 na kayayyakin da suke sayar mata; Kazalika, kasar Sin za ta bada kudin karo-karo da yawansu ya kai dalloli miliyan 30 ga kungiyar samar da abinci ta MDD wajen kafa wata asusun lamuni da zummar taimakon kasashe masu tasowa wajen yin aikin gona.
Sa'annan Mista Wen Jiabao ya gabatar da wassu sahihan shawarwari. Yana mai cewa: "Na bada shawarar kara samar da gudummowa ga gamayyar kasa da kasa, musamman ma kasashe masu cigaba su dauki nauyin taimakon kasashe marasa ci gaba".
1 2 3
|