A shekarar 2003 da kuma ta 2005, kasar Sin ta taba gudanar da ayyukan tafiyar da kumbo da ke dauke da 'yan sama jannati har sau biyu. Mr. Wang Zhaoyao ya ce, idan aka kwatanta wannan karo da lokuta biyu da suka gabata, ana iya ganin cewa, za a gamu da kabulale da ba a taba ganin irinsa ba wajen fitar da 'yan sama jannati daga kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' a wannan karo. Game da haka, Mr. Wang Zhaoyao ya ce,
'A yayin da ake tafiyar da wannan kumbo, wani 'dan sama jannati zai fita daga kumbo, domin tattara na'urorin gwaje gwaje da aka kafa a wajen kumbon.'
1 2 3
|