Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-24 18:10:00    
Kasar Sin za ta harba kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' da ke dauke da 'yan sama jannati a ran 25 ga wata da dare

cri

A ran 24 ga wata a cibiyar harba tauraron 'dan adam ta Jiuquan, kakakin ayyukan tafiyar da kumbuna da ke dauke da 'yan sama jannati na kasar Sin Mr. Wang Zhaoyao ya sanar da cewa, kasar Sin za ta harba kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' da ke dauke da 'yan sama jannati a ran 25 ga wata da dare. Za a harba kumbo ne da ke dauke da 'yan sama jannati uku, wadanda za su fita daga kumbo domin gudanar da ayyuka a karo na farko. Mr. Wang ya ce,

'Babban makasudi na wannan aiki na tafiyar da kumbo a wannan karo shi ne domin 'yan sama jannati su fita daga kumbo, da kuma yin nazari da sanin fasahohin da abin ya shafa wajen fita daga kumbo a sararin samaniya. A sa'i daya kuma, za a yi gwaje gwaje game da tafiyar da tauraron 'dan Adam tare da kumbo, da kuma yin nazari kan jigilar labarai tsakanin tauraron 'dan Adam da kumbo. 'Yan sama jannati uku za su gudanar da wannan aiki. Bisa shirin da aka yi, an ce, za a harba kumbo ne daga filin harba kumbuna na cibiyar harba tauraron 'dan adam ta Jiuquan.'


1 2 3