Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-09 16:56:53    
'Yan wasa na kasar Afirka ta kudu sun nuna gwanintarsu a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing

cri

Ba ma kawai madam Natalie Du Toit ta samu maki mai kyau a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ba, har ma wani dan wasa na kasar Afirka ta kudu daban ya samu maki mai kyau. Wannan dan wasa shi ne Oscar Pistorius wanda ake kiran shi "sojan kaifin wuka" kuma ya kware sosai kan wasan ninkayya na mita 100 na ajin na T44. A gun gasar wasan ninkayya ta mita 100 da aka yi a ran 8 ga wata da dare, Oscar Pistorius bai yi kasa a guiwa ba ga burin jama'a, cikin sauki ne ya samu izinin shiga gasar karshe da za a yi a ran 9 ga wata da dare.

Oscar Pistorius wanda ya kasa kafafunsa lokacin da yake karami bai kasa kishinsa kan wasannin motsa jiki ba. Ya kan zama zakara a gun gasannin da aka shirya a kasar Afirka ta kudu domin 'yan wasa marasa nakasa, kuma ya zama mutum marasa kafafu da ya yi gudu mafi sauri a nan duniya. Kafin ya shiga gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, ya riga ya karya matsayin bajinta na nakasassu na duniya har sau 26. Lokacin da yake ganawa da wakilanmu a ran 8 ga wata dare, Oscar Pistorius yana cike da imani ga gasar karshe da za a yi a ran 9 ga wata da dare, ya ce, "Ina fatan zan iya samun makin da ba zai kai dakika 11 ba a gun gasar da za a yi gobe, wannan kuma buri ne da nake son cimmawa yau da dare. Amma ba damuwa, ina tsammani lokacin da nake gasa da Brian Frasure gobe, mai yiyuwa ne zan iya samun makin da ba zai kai dakika 11 ba."


1 2 3 4