Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-09 16:56:53    
'Yan wasa na kasar Afirka ta kudu sun nuna gwanintarsu a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing

cri

Ko da yake madam Natalie ta soma yin gasa tare da 'yan wasa marasa nakasa a gun gasar wasannin motsa jiki na kungiyar Commonwealth ta shekara ta 2002. Amma madam Natalie tana ganin cewa, a hakika dai, shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing yana canja zaman rayuwarta. "Yanzu manema labaru da yawa suna son yin intabiyu da ni. Kuma ina kokarin mai da hankalina kan kowane intabiyu. Ina son gaya wa abokaina cewa, da kuna da mafarki, tabbas ne za ku iya cimmawa, amma sharadin cimma burinku shi ne dole ne kun yi namijin kokari."

Sabo da madam Natalie Du Toit tana matsayin wakiliyar nuna alamun kayayyakin da ake samarwa a gasar wasannin Olympic ta Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, bayan da aka rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing, bisa gayyatar da aka yi mata ne, ta ci gaba da zama a nan Beijing domin jiran gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. A cikin wannan lokaci, ta mayar da hankalinta kan gasar wasannin Olympic ta nakasassu daga gasar wasannin Olympic ta Beijing cikin sauri. Kuma abin da take jin mamaki shi ne a gun gasannin da aka yi a rana ta farko, ta samu wata lambar zinariya da wata lambar azurfa. Madam Natalie tana farin ciki sosai, ta ce, "Ina jin mamaki kwarai na karya matsayin bajinta na duniya a gun gasar da aka yi a rana ta farko. Wannan abu ne da nake farin ciki, kuma shi wani maki ne da ke karfafa gwiwata."


1 2 3 4