Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 12:35:45    
Yaushe gwamnatin Amurka ta warware matsalar gidaje ?

cri

Manazarta harkokin duniya na yau da kullum suna masu ra'ayin cewa a wannan lokaci gwamnatin Amurka ta ba da sanarwar karbi hukumomin nan biyu masu ba da lamuni ga masu saye gidaje ne,a galibi dai tana so ta kwantar da hankalin mutane maimakon ta shiga tsaka mai wuya. Tun farkon shekarar bana da akwai bankuna goma da suka rufe kofofinsu a Amurka,,wannan ya raunana niyyar masu zuba jari. Faduwar farashin gidajen da ake yi ta sa masaye gidaje masu karin yawa ba su da karfin biyan bashi.baki masu zuba jari suna damuwa ba za su tsinana kome ba sabo da rikicin kudin da hukumomin nan biyu na Amurka ke faam da shi. Hukumomin nan biyu masu ba da lamuni ga masaye gidaje sun gaza fitar da kansu daga halin kangin da suka sami kansu a ciki saboda manyan basussuka da suka ci.

Wannan dalili ne da ya sa gwamnati ta gaggauta ta sa hannu a kai,wani dalili daban da gwamnatin Amurka ta sa hannu a kai shi ne,hukumar Morgan Stanley,hukumar ba da shawarwari kan kudi da ma'aikatar kudi ta Amurka ta dauka ta bayyana cewa ta gano matsaloli da dama a hukumomin nan biyu masu ba da lamuni bayan da ta yi musu binciken kudi kan takardunsu da aka tanada kmar su yin magudi da bayar da bayanan jabu.Mr Paulson ya bayyana cewa an dauki mataki a wannan lokaci dalili kuwa shi ne hukumar Fannie Mae da hukumar Freddie Mac suna kasance manyan hukumomi dake da nasaba sarkakkiya a kasuwar kudi,idan wani reshe ya rushe zai haddasa babban rikicin kudi a kasuwar kudi ta Amurka da ta duniya baki daya. Shugaban kwamitin kula da harkokin kudi na ma'aikatar harkokin waje ta Amurka Mr Barney Frank ya bayyana cewa halin da hukumomin nan biyu ke ciki bai kai rushewarsu nan da nan ba,gwamnatin ta dauki wannan mataki ne duk domin kwantar da hankalin mutane da maganin rikici a kasuwar kudi.


1 2 3