Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 12:35:45    
Yaushe gwamnatin Amurka ta warware matsalar gidaje ?

cri

Yayin da kasuwar ba da lamuni ga masu saye gidaje ta Amurka ta kara dagula, da kuma farashin hannayen jari na muhimman hukumomin ba da lamuni ga masu saye gidaje wato Fannie Mae da Freddie Mac na kara faduwa,gwamnatin Amurka a ran 7 ga wata bisa agogon wurin ta bayyana cewa za ta kula da hukumomin nan biyu cikin dan lokaci duk domin zaunar da kasuwar bad a lamuni ga masu saye gidaje da kuma maganin rikicin kudin da zai yiwu faruwa. Wannan muhimmin mataki ne da gwamnatin Amurka ta dauka wajen ba da agaji ga hukumomin ba da lamuni da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Amurka. Ko cause za a warware wannan matsalar da ake fama da ita a Amurka dangane da hukumomin biyu masu bad a lamuni ga masu saye gidaje.sai a jira a ga gwamnatin Amurka ta sabon wa'adi mai zuwa.

Hukumar Fannier Mae da hukumar Freddie Mac,muhimman hukumomi biyu ne na ba da lamuni ga masu saye gidaje a Amurka. Muhimman harkokinsu su ne su saye lamuni mai karancin ruwa da bankunan suka bayar ga masu saye gidaje,su hada shi da sauran harkokinsu sannan su mai da su takardun shaidu su sayar da su ga masu saye gidaje. Darajar kudin takardun shaidu da hukumomin nan biyu ke da su ta kai kudin daalr Amurka biliyan dubu biyar,wato ta kai kusan rabin kasuwar ba da lamuni ta kasar Amurka na dalar biliyan 1200. Ban da wannan kuma darajar takardun kudin da sassan bankin tsakiya da sauran hukumomin kudade ke da su ta kai dalar Amurka biliyan 130.dadin dadawa, tun lokacin da aka fara samun matsalar ba da lamuni ga masu saye gidaje,farashin hananayen jari na hukumomin nan biyu ya ragu da kashi casa'in bisa dari,wato sun yi hassarar dakar Amurka biliyan 14,da wuya a kimanta yawan hassara da za su samu a nan gaba. Idan manyan hukumomin nan biyu na Amurka su rushe,ba ma kawai sun zama babbar masifa ga tattalin arzikin Amurka,hatta ma za su kawo mugun lahani ga kasuwar kudi ta duniya.To ta yaya za a kubutar da hukumomin nan biyu na Amurka gwamnatin Amurka ta zuba ido kan batun nan cikin watannin baya. Ministan kudi na Amurka Henry Paulson ya ce gwamnatin ba za ta dauki matakin riko ba sai a lokaci da ya wajaba.


1 2 3