Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-29 16:12:55    
Sansanin matasa na Olympics na birnin Beijing

cri

Bayan da suka shafe kwanaki 12 suna zama cikin sansanin, 'yan sansani sun zurfafa fahimtarsu a kan "duniya daya, buri daya", Losel Thupton, wani yaron da ya zo daga kasar Bhutan, ya ce, "launin fatanmu daban daban ne, kuma mun zo daga iyalai daban daban da kuma kabilu daban daban, amma muna da duniya daya ne kawai, da kuma buri daya, wato zaman lafiya, da manufar wasannin Olympics, da kuma zumuncin da mu'amala da ke tsakanin jama'ar kasashe daban daban."

Lokacin da muka je wannan sansanin matasa, rana ce ta karshe da aka gudanar da sansanin, kuma abin da muka gani a wurin ya burge mu kwarai da gaske. Matasa masu launuka daban daban sun rungumi juna, sun yi ta daukar hotuna da juna, suna sanya sunayensu a kan riguna da littattafan juna. Vasile Marina Gabriela, wata yariyar da ta zo daga kasar Romania, ta ce, "Ina son Beijing, ta burge ni sosai. 'Beijing' ta kuma kasance kalmar Sinanci ta farko da na koyi rubutunsa a nan, wannan sansani yana da kyau da ban sha'awa. Na sami abokai daga kasashe daban daban, yanzu sun kasance tamkar iyalaina, ina sonsu duka, ba na son yin ban kwana da su. Yau da dare na yi bakin ciki, ba na son bar nan, amma zaman rayuwa haka yake. Ina fatan zan iya sake haduwa da su a birnin London."

Lokacin ban kwana ya yi, matasan suna rungumar juna, da Sinancin da suka koya ne suna ta cewa, "Beijing, sai wata rana", da kuma "duniya daya, buri daya." (Lubabatu)


1 2 3