Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-29 16:12:55    
Sansanin matasa na Olympics na birnin Beijing

cri

An dai gudanar da harkokin sansani a fannoni uku, wato "kallon wasannin Olympics" da "mu'amala da juna" da kuma "fahimtar kasar Sin", inda matasa kusan 500 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi sama da 200 suka hadu a nan birnin Beijing, suka halarci bikin fara wasannin Olympics da kallon wasannin Olympics da yin mu'amala da juna da kuma ziyartar ni'imtattun wurare masu tarihi a nan birnin Beijing. A cikin wadannan kwanaki 12, matasan sun kara fahimtar juna da kuma kulla zumunci da juna.

A yayin da yake hira da mu, Mudassir Umar, wanda ya zo daga kasar Nijeriya, ya ce, a cikin kwanakin nan 12, ya sami abokai daga kasashe da shiyyoyi daban daban. Ya ce, "Na samu abokai gaskiya da dama, na samu daga Fiji da Puerto Rico da New Zealand da Brazil da Portugal da dai sauransu, mun zauna lafiya da juna, an yi wasa da dariya, na ji dadin zama."

Mudassir Umar ya ce, ta zama tare da kallon wasanni tare da shiga mota daya da yin hira tare da wasa da dariya da kuma cin abinci tare, sun kara fahimtar juna. Ga shi, ya kuma koyi wasu sabbin abubuwan da bai sani ba daga abokansa. Ya ce, "Na zo na ga yaren da ban sani ba, na koyi kalmomi da dama, a yaren Fiji, aka ce 'ora', ana nufin mai kyau ke nan da mace, in aka ce 'suna' wato mai kyau daga namiji ke nan. A kasar Sin kuma, in aka ce, "wo ai ni", ana nufin "I love you", kin ga na ji abin da ban sani ba ke nan, da dai sauransu. sa'an nan, mu kan zauna da juna, sun nuna mana abin da ba mu sani ba, mun karu, mun nuna musu abin da ba su sani ba."

Jama'a, babban taken na wasannin Olympics na Beijing shi ne "duniya daya, buri daya", kuma sansanin matasan Olympic da aka gudanar a wannan karo shi ma ya bayyana wannan take. Mr.Yang Xuelun, mataimakin shugaban kula da dakunan sansanin, ya ce, "Babban taken wasannin Olympics na Beijing shi ne 'duniya daya, buri daya', kuma taken sansaninmu shi ne 'matasa suna kirkiro makomar duniya', a hakika, wannan take na biye da babban taken wasannin Olympics na Beijing, wato ma'anarsu daya ne, wato matasan duniya suna da makoma iri daya da kuma kyakkyawan buri daya."

Mr.Yang Xuelun ya ce, an sanya matasa da suka zo daga kabilu da wurare daban daban, wadanda ke da al'adu da addinai daban daban, a cikin rukuni daya, don ba su damar kara fahimtar juna, kuma buri shi ne a kawar da rashin fahimtar juna har kiyayya da juna a tsakanin kabilu daban daban, a yi kokarin neman samun zaman lafiya da cigaba da kuma albarka a duniya.


1 2 3