Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-29 16:12:55    
Sansanin matasa na Olympics na birnin Beijing

cri

A ran 17 ga watan nan da muke ciki, aka kawo karshen sansanin matasa na Olympics na birnin Beijing, wanda aka shafe kwanaki 12 ana gudanar da shi.

A shekaru dari da suka wuce, Pierre De Coubertin, uban wasannin Olympics na zamani ya taba bayyana cewa, wasannin Olympics na iya samar wa matasan duniya wata damar haduwa a gu daya cikin farin ciki tamkar 'yan uwa daya. To, tun daga wancan lokaci ne, musamman ma daga sansanin matasa Olympics da aka fara gudanarwa a gun wasannin Olympics a birnin Stockholm a shekarar 1912, an hada wasannin Olympic da matasa na kasashe daban daban a gu daya.

A gun bikin rufe sansanin matasa na Olympics na wannan karo da aka gudanar a ran 17 ga wata da dare, shugaban sashen kula da harkokin al'adu na kwamitin wasannin Olympics na Beijing kuma babban sakataren kwamitin sansanin, Mr.Zhao Dongming ya yi jawabin cewa, "Da sahihiyar zuciya ce nake fatan kowane dan sansanin zai iya kasancewa da himma a wasannin Olympics, da zumunci, domin zaman lafiya da hadin gwiwa da kuma cigaba a nahiyoyi biyar na duniya."


1 2 3