
Benjamin Boukpeti 'dan shekaru 27 yana wasan kwale kwale na Kayak Salalom har shekaru 15, maki mafi kyau da ya samu kafin wannan shi ne, ya zo na farko a gasar neman damar shiga wasannin Olympics a yankin Afrika, da ta shiga wasan cin kofi na Afrika. A gun gasar wasannin Olympics da aka shirya a shekaru hudu da suka wuce a Athens, ko da ya ke Benjamin Boukpeti ya shiga gasar karshe, amma ya zo na 18 kawai.
Ko da ya ke ya samu lambar tagulla kawai a gasar karshe a wasannin Olympics na Beijing, amma Benjamin Boukpeti ya nuna kwarewarsa sosai a gun wasannin, har ma ya taba zaman lambawan bayan da aka kammala gasar kusa da na karshe.
"Lallai na yi mamaki sosai kan sakamakon da na samu a gasar kusa da na karshe, ban san me ya faru kan sauran 'yan wasa ba, a ganina ko da ya ke na nuna kwarewata, amma ba cikakkiyar kwarewa ba, saboda haka, ina tsamani zan zo na hudu ko biyar, amma a karshe dai na samu lambawan."
Saboda mamar Benjamin Boukpeti ta zo daga kasar Faransa, kuma babansa 'dan kasar Togo ne, don haka, a waje daya ne Benjamin Boukpeti da 'dan uwansa Olivier Boukpeti suna da iznin zama a Faransa da na Togo. Amma, a lokacin da suke zaben kasar da za su wakilta, 'yan uwan biyu suna da ra'yoyi daban daban kan wannan. 'Dan uwansa ya zabi kasar Faransa, Benjamin Boukpeti kuma ya zabi kasar Togo. Kan wannan zaben da ya yi, Benjamin Boukpeti ya ce,
"Ko da ya ke ina zama a kasar Fransa, amma na iya yin mu'ammala tare da kasar Togo ta hanyar daban daban. Bayan haka kuma, ina ganin cewa, ina daga kasar Togo a cikin zuciyata, a kalla dai wasu abubuwana suna cikin kasar Togo, gaskiya ne, ba na iya yin watsi da al'adu na kasar, da kuma kome da kome na kasar, lallai na yi farin ciki sosai saboda na iya cimma burina ta hanyar wasannin Olympics."
1 2 3
|