Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-28 15:48:00    
Benjamin Boukpeti, wanda ya samu lambar yabo ta farko ta wasannin Olympics ga kasar Togo

cri

A gun gasar wasannin Olympics da aka kammala ba da dadewa ba a nan birnin Beijing, wasu kasashe sun samu lambar yabo ta farko a tarihinsu, ciki har da kasar Togo daga Afrika. Kwanan baya, wakilinmu ya kai ziyara ga Benjamin Boukpeti, wato 'dan wasan da ya samu wannan lambar yabo mai ma'ana sosai ga kasar Togo a gasar kwale kwale na Kayak Slalom. Yanzu kuma bari mu ga cikakken bayanin.

Fadin kasar Togo da ke yammacin Afrika ya kai muraba'in kilomita dubu 60, yawan mutanen kasar bai wuce miliyan 6.5 ba. Tun daga shekarar 1972, kasar Togo ta soma aikawa da kungiar wasannin motsa jiki don shiga wasannin Olympics, amma kafin gasar wasannin Olympics ta Beijing ba ta taba samun lambar yabo ko daya tak ba. A shekarar da muke ciki, akwai 'yan wasa hudu daga kasar Togo da suka shiga wasannin Olympics na Beijing, ciki kuwa Benjamin Boukpeti ya samu lambar tagulla a gasar kwale kwale na Kayak Salalom. Kan wannan lambar yabo da aka samu ba cikin sauki ba, shugaban kungiyar wasannin mota jiki ta kasar Togo Lawson Hellu Akuele ya yi farin ciki sosai, ya ce,

"Lallai mun yi mamaki sosai kan wannan lambar yabo ta farko da muka samu a tarihin kasar Togo. A hakika dai, 'yan wasan kungiyarmu ba su fahimci juna ba kafin mu zo nan birnin Beijing, amma yanzu muna kamar zama a wani iyali daya. Wannan na da ma'ana sosai, musamman ma ga Benjamin Boukpeti, saboda a ranar 4 ga wata, mun shirya masa wani bikin musamman, don taya murnar ranar shekarun haihuwarsa, dukkanmu mun kasance cikin sakin jiki sosai, kuma mun yi hadin gwiwa sosai a kungiyarmu. Daga baya kuma, ya samu wata lambar tagulla, wannan lambar yabo ta farko ce da kasarmu ta samu a tarihi, gaskiya ne, mun yi farin ciki sosai."


1 2 3