Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 17:14:17    
Rasha ta amince da 'yancin Ossetia ta kudu da Abkhazia

cri

A waje daya kuma, kudurin shugaban Rasha ya jawo hankulan kasashen yammacin duniya sosai. Madam Condoleeza Rice wadda ke kula da harkokin waje a cikin gwamnatin kasar Amurka ta nuna bakin ciki ga kudurin amincewa da 'yancin Ossetia ta kudu da Abkhazia da kasar Rasha ta yi. Ta jaddada cewa, kasar Amurka za ta ci gaba da amincewa da kasancewar yankunan Ossetia ta kudu da Abkhazia yankuna ne na kasar Georgia, kuma tana shirin amfani da "ikon nuna adawa" a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya domin hana yunkurin canja halin da ake ciki da kasar Rasha take yi. Sannan, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce, ba a iya amincewa da kudurin Rasha ba kwata kwata sabo da "ya karya ka'idojin kasashen duniya". A waje daya kuma, David Miliband, ministan harkokin waje na kasar Britaniya ya ce, kasar Rasha ba ta da dalilin amincewa da 'yancin Ossetia ta kudu da Abkhazia, kuma ba za a iya amincewa da wannan kuduri ba, har ma ya nemi a kafa wata kawancen nuna adawa da "kasar Rasha ta kai hari kan kasar Georgia". Bugu da kari kuma, shugaban kasar Faransa, kuma shugaban wannan zagaye na kungiyar tarayyar Turai Nicolas Sarkozy da ministan harkokin waje na kasar Faransa Bernard Kouchner sun nuna bakin ciki, kuma sun zargi matakin da kasar Rasha ta dauka.

Bisa labarin da hukumar yada labaru ta fadar Krimlin ta kasar Rasha ta bayar, an ce, yanzu shugaba Medvedev ya riga ya nemi ma'aikakar harkokin waje da sauran hukumomin da abin ya shafa na Rasha da su yi shawarwari da bangarorin Abkhazia da Ossetia ta kudu kan batun kafa huldar diplomasiyya a tsakaninsu da kasar Rasha, a waje daya kuma, ya neme su da su tattauna batun kulla takardar sada zumunta a tsakanin Rasha da Ossetia ta kudu da Abkhazia. Bugu da kari kuma, Mr. Vitaliy Churkin, zaunannen wakilin kasar Rasha da ke majalisar dinkin duniya ya sanar da cewa, kasar Rasha ta riga ta sanar wa babban sakataren majalisar dinkin duniya da wannan kudurin amincewa da 'yancin Ossetia ta kudu da Abkhazia.  (Sanusi Chen)


1 2 3