Kafin wannan rana, majalisun kafa dokokin kasar Rasha biyu dukkansu sun yarda da nuna goyon baya ga 'yancin kan Ossetia ta kudu da Abkhazia. Sun kuma nemi shugaban kasar Rasha da sauran kasashen duniya da su yi nazari kan batun 'yancin Abkhazia da Ossetia ta kudu. Bisa wannan kiran da aka yi ne, Mr. Medvedev ya tsai da kudurin amincewa da 'yancin Ossetia da Abkhazia.
Bayan da shugaban kasar Rasha ya sanar da amincewa da 'yancin Ossetia ta kudu da Abkhazia, bangaren Georgia ya mai da martani cikin farkon lokaci. Nan da nan ne shugaban kasar Georgia ya kira taron kwamitin tsaron kasar domin tattaunawar wannan batu. A gun wata hirar da ya yi da wakilin gidan rediyon Echo na kasar Rasha, Mr. Alexander Lomaya, sakataren kwamitin tsaron kasar Georgia ya ce, za a karya huldar da ke tsakanin Georgia da Rasha har abada. Wani mataimakin ministan harkokin waje na kasar Georgia ya ce, matakin da bangaren Rasha ya dauka mataki ne da ke "cin yankunan Georgia a fili".
1 2 3
|