Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 17:14:17    
Rasha ta amince da 'yancin Ossetia ta kudu da Abkhazia

cri

A ran 26 ga wata, shugaban kasar Rasha Dmitri Medvedev ya sa hannu kan wani umurnin shugaban kasar, inda ya amince da 'yancin kan yankin Ossetia ta kudu da yankin Abkhazia. Nan da nan ne kasashen yammacin duniya sun mai da martani da kakkausar harshe kan wannan kudurin shugaban kasar Rasha.

A cikin wata sanarwar da Mr. Medvedev ya bayar a wannan rana, ya ce, bisa fatan jama'ar Ossetia ta kudu da Abkhazia da kundin majalisar dinkin duniya da ka'idojin dokar kasa da kasa da ke shafar huldar sada zumunta a tsakanin kasa da kasa da aka tsara a shekarar 1970 da takardar Helsinki da kwamitin tsaron Turai ya kulla a shekarar 1975 da ka'idojin sauran takardun kasashen duniya, ya rattaba hannu kan umurnin da Tarayyar Rasha ta amince da 'yancin yankunan Ossetia ta kudu da Abkhazia. Wannan sanarwa ta ce, wannan zabi ne ba na sauki ba, amma wannan zabi kadai ne da zai tabbatar da rayukan jama'a. Kasar Rasha ta yi kira ga sauran kasashen duniya da su bi wannan ka'idar da ake bi.


1 2 3