Idan ana son yi wa gasar wasannin Olimpic kirari, kuma ya kamata a yi wa birnin da ya shirya wannan gasar wasannin Olimpic wato Beijing kirari, da yi wa jama'a masu yawan biliyan 1.3 na kasar Sin, kasa mai masaukin gasar kirari!
Cikin gajeren lokaci na kwanaki 16 kawai da suka wuce, an gudanar da babban batun "Duniya daya, nufi daya" a gun gasar wasannin Olimpic, don haka an tabbatar da babbar manufar "sigar musamman da matsayi mai kyau" ta gasar tare da nasara, da yada tunani 3 na gasar wato "tsabtataccen wasannin Olimpic na kimiyya da fasaha, kuma na zamantakewar al'adu".
Mr. Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olimpic na kasashen duniya ya bayyana cewa, abu mafi ma'ana da gasar wasannin Olimpic ta Beijing ta bari shi ne, "Ta hanyar yin wannan gasar wasannin Olimpic, duniya ta kara fahintar kasar Sin, kasar Sin kuma ta kara fahintar duniya." (Umaru) 1 2 3
|