Idan ana son yi wa gasar wasannin Olimpic kirari, ya kamata a yi wa tunanin wasannin Olimpic wato "kara sama, kara sauri, kuma kara karfi" kirari!
A gun bikin rufe gasar, Mr. Liu Qi, shugaban kwamitin shirya wasannin Olipic na Beijing ya bayyana cewa, "Cikin kwanaki 16 da suka wuce, 'yan wasan motsa jiki da suka zo daga kasashe da bangarori 204 na duniya sun yada tunanin Olimpic, cikin gasannin da suka yi sun nuna halin gagara badau kuma bisa adalci, sun fid da gwani kuma sun nuna halin nagari wajen gasar, sun kago nasarori masu faranta ran mutane, sun karya matsayin bajinta na duniya har sau 38, da matsayin bajinta na Olimpic har sau 85."
A gun gasar wasannin Olimpic na Beijing, kasashe da yawa sun tabbatar da mafarkinsu na samun lambobin yabo na wasannin Olimpic.
Idan ana son yi wa gasar wasannin Olimpic kirari, ya kamata a yi wa tunanin wasannin Olimpic wato "zaman lafiya, da hadin kai, da zumunci da ci gaba" kirari!
"Zaman lafiya, da hadin kai, da zumunci da ci gaba" manufar wasannin Olimpic ce da marigayi Lebaron Pierre De Coubertin, madugun wasannin Olimpic na zamani ya gabatar, ita ba ma kawai ta zama kwayar tunanin al'adu na Olimpic ba, har ma tana wakiltar manufar tarayya da duk 'yan adam ke neman tabbatar da ita.
1 2 3
|