Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-25 18:35:36    
An yi wa gasar wasannin Olimpic kirari

cri

A ran 24 ga wata da dare na agogon birnin Beijing, an sake rera wakar wasannin Olimpic a filin wasan motsa jiki na kasa mai siffar sheka da ke nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, kuma an yi kirarin farin ciki domin kawo karshen gasar wasannin Olimpic na yanayin zafi na 29 wadda aka shafe kwanaki 16 ana yin ta.

"Ina nuna godiya ga kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing, wannan gasar wasannin Olimpic wata gasar wasannin Olimpic ce ta gaskiya wadda ba safai akan ganin irin ta a tarihi ba."

Maganar nan ta zama yabo ne da Mr. Jacgues Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olimpic na kasashen duniya ya yi wa gasar wasannin Olimpic ta Beijing da sahihiyar zuciya.

Cikin wadannan kwanaki 16, duk duniya ta nuna sha'awa sosai ga wasannin Olimpic da aka shirya a nan birnin Beijing, haka ma ta nuna sha'awa sosai ga birnin Beijing. Sabo da haka, bari mu yi wa gasar wasannin Olimpic kirari!


1 2 3