Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 15:07:19    
Wasan kwallon kwando na maza tsakanin Sin da Amurka

cri

Kasar Amurka ta fi karfi a wasan kwallon kwando na maza,kasar Sin ba ta kai wannan matsayi ba,ta taba shiga jeren kasashe takwas a gaba a wannan wasan kwallon kwando a tarihinta.da ake yin gasa,kwararru 'yan wasa na duniya a wannan fanni kamar su Yao Ming da Kobe Bryant da Lebron James sun shiga gasar. A cikin shekarun baya, kasar Sin da Amurka sun sha yin mu'amala a wasan kwallon kwando, shi ya sa gasar nan tana ma'ana ta musamman. Shugaban kungiyar 'yan wasa ta Amurka Mr Mike Krzyzewski ya ce "kungiyar 'yan wasa ta kasar Sin,kungiyar abokan gaba ce tamu ta farko a wannan wasannin Olympics, a ganina babu gasa da ta fi wannan sha'awa,a yi gasa a karo na farko da kungiyar kasar Sin a yankin kasar Sin,babbar alfarma ce gare mu."

Wannan gasar ta samu 'yan kallo masu kishin wasan kwallon kwand masu yawan gasket. Da ya ke karfin kungiyoyin kasashen nan biyu ya sha banban da juna,kungiyar Amurka ta kan kai hari ga kungiyar kasar Sin a karshen karo, 'yan kallo masu kishin wasan kwallon kwando na kasar Sin ba ma kawai sun sa kaimi ga kungiyar kasar Sin kawai ba har ma sun sa kaimi ga kungiyar Amurka,an gudana da gasar cikin fara'a da farin ciki. Dan jarida na gidan talabiji ESPN a wasannin motsa jiki na Amurka Mr Smith ya bayyana cewa " bisa labarin da muka samu, an ce wannan gasa ta sami 'yan kallo fiye da biliyan daya a duniya,da mun sanar da labarin ga 'yan wasa na Amurka dukkansu sun jiku sosai,dalili kuwa shi ne wannan gasa ta samu 'yan kallo mafi yawa a tarihi.A kowane lungun filin gasa,kana iya jin sha'awa da 'yan kallo masu kishin wasan kwallon kwando suka nuna.

Da dan wasa Yao Ming da sauran 'yan wasa na kasar Sin suka shiga filin wasan,'yan kallo suka tashi sun yi tafi mai yawa suna ihu,haka ma sun nuna wa dan wasa Kobe Bryant da sauran 'yan wasa na Amurka da suka shiga filin wasan,wakilin gidan rediyonmu ya girgiza kan sha'awa da 'yan kallo suka nuna a filin. Mr Wang Xiaojie,mai kula da shirye shiryen "wasannin Olympics" na gidan talabiji na tsakiya na kasar Sin shi ma yana da wannan ra'ayi. Ya ce " ba mu iya gane wace kungiya ta dama,wace ta hagu, da dan wasan kungiyar Amurka ya sa kwallo a cikin kwando,'yan kallo na kasar Sin sun yi masa kuwa da tafi da sa masa kaimi.


1 2 3