Ko da yake Mr. Nobre ya yi ta jaddada cewa, a maimakon samun lambobin yabo, Benin ta mai da hankali kan shiga gasanni kawai a wannan karo. Amma a matsayinta na wata 'yar wasa, musamman ma a matsayinta mai rike da tutar kasa na kungiyar wakilai na Benin, Fabienne Fereaz, wata magujiya ta tsawon mita 200 tana ganin cewa, samun maki mai kyau a cikin gasa, shi ne nauyi da aka danka wa wani dan wasa. Ta ce,'Zan yi kokari sosai domin shiga gasar karon karshe. Yanzu ya rage kwanaki kadan da bude gasar, shi ya sa ban daina aikin horo ba sai a shirye nake yi.'
A idon wannan budurwa da ta kawo wa kasar Sin ziyara a karo na farko, kasar Sin da ke gabashin duniya mai dogon tarihi ta jawo hankalinta sosai. A lokacin hutu, kamar yadda sauran 'yan wasa suke yi, za ta kara fahimta kan al'adun kasar Sin a lokacin da take nan kasar Sin. Ta gaya mana cewa,'A lokacin gudanar da gasar wasannin Olympic, ina son in kai ziyara ga babbar ganuwa ta kasar Sin wato the Great Wall da kuma fadar sarakuna ta kasar Sin wato Forbidden City. Galibi dai, ina fatan zan iya kai ziyara ga karin wurare na kasar Sin.'(Tasallah) 1 2 3
|