Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 19:40:09    
Benin ta zama ta farko a tsakanin dukkan kungiyoyin wakilai na kasashen waje wajen shirya bikin daga tutarta a kauyen wasannin Olympic

cri

Kasar Benin da ke yammacin Afirka tana da mutane miliyan 6 ko fiye, ba ta nuna karfi sosai a wasannin motsa jiki ba, amma mutanen Benin suna matukar kishin wasannin motsa jiki da wasannin Olympic. A shekarar 1960 ne aka kafa kasar Benin, bayan shekaru 2, ta shiga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, ta kuma halarci gasar wasannin Olympics sau 8 a jere tun daga shekarar 1972. Charles Nobre, shugaban kungiyar wakilai ta Benin a wannan karo ya taba shiga gasar wasannin Olympic sau 7, ya fahimci ruhun wasannin Olympic sosai. Ya gaya mana cewa,'A ganina, baya ga samun lambobin zinariya da samun nasara, gasar wasannin Olympic na kasancewa wani kasaitaccen biki da aka tabbatar da jituwa a tsakanin 'yan Adam. Ina fatan, gasar wasannin Olympic za ta kawo wa dukkan kasashe da yankuna na duniya zaman lafiya da kwanciyar hankali, gasar wasannin Olympic za ta hada jama'ar duniya tare. Dukkanmu za mu zama 'yan uwa.'

An labarta cewa, kungiyar wakilai ta Benin da ta shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing ta hada da mutane 14, ciki har da 'yan wasa 5. Game da wadannan 'yan wasa, Olivia Anana, jami'ar kwamitin wasannin Olympic na Benin mai kula da ba da hidima ta yi karin bayani da cewa,''Yan wasanmu za su shiga gasannin guje-guje da tsalle-tsalle da wasan ninkaya da wasan Taekwondo. Ko da yake an sami asalin wasan Taekwondo a Asiya, amma 'yan wasanmu sun dade suna karatu da yin aikin horo a kasar Korea ta Kudu, sun horar da kansu kamar yadda sauran 'yan wasanmu suke yi.'


1 2 3