Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 15:59:38    
Cin gasassun agwagi irin na Beijing

cri

 

A kwanan baya, dakin cin abinci na Quanjude ya yi wa rassansu kwaskwarima domin karbar karin masu cin abinci. Sa'an nan kuma, ya horar da sabis a fannonin da abin ya shafa, ya kuma yi kokarin kyautata matsayinsu a fannonin tuntubar masu cin abinci cikin Turanci da kuma ba da hidima.

Dakin cin abinci na Quanjude yana fatan ko wane mai cin abinci zai fahimci Sinawab da ke son baki da kuma dumama zukatunsu. Baya ga Turanci, sabis da ke aiki a cikin wannan dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi sun kuma koyi al'adun gargajiya da ake bi a yankuna da kasashe na duk duniya da kuma abubuwan kunya, har ma da yin magana ta hanyar alamu.

Yanzu abincin kwalama suna samun saurin bunkasuwa, amma duk da haka ana ci gaba da gasa agwagi ta hanyar gargajiya wajen samar da gasassun agwagi irin na Beijing. Ana samun karin dakunan cin abinci da suka yi kama da dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi mai suna Quanjude a Beijing. Dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi mai suna Dadong na daya daga cikin irin wadannan dakunan cin abinci, shi ma ya fara kafa rassansa a Beijing. Chen Qianzhu, wata kwararriya ce a fannin al'adun abinci. Dangane da irin wadannan dakunan cin abinci na sayar da gasassun agwagi, ta bayyana ra'ayinta bayan da ta kwatanta su. Ta ce,'Dakin cin abinci na Dadong ya fi mai da hankali kan biyan bukatun mutanen kasashen waje, ko da yake ya bi hanyar gargajiya wajen gasa agwagi, amma ya nuna bambanci a naman agwagi. A ganina, naman gasassun agwagi da ake samarwa a dakin cin abinci na Dadong yana da dadin ci sosai kamar yadda naman gasassun agwagi da ake samarwa a dakin cin abinci na Quanjude yake.'

Kazalika kuma, wannan kwararriya ta gabatar wa masu sauraronmu da wasu dakunan cin abinci da suka gasa agwagi ta sabbin hanyoyi. Ta gaya mana cewa, wadannan sabbin dakunan cin abinci sun mai da hankulansu kan wuraren da za su samarwa masu cin abinci, sun kuma kayatar da kansu ta hanyoyin musamman, ta haka, matafiya daga kasashen waje sun iya gane bambanci. Madam Chen ta ce,'Akwai wani dakin cin abinci mai suna Quanyaji, inda aka gasa agwagi da yawa. Sa'an nan kuma, wurin da aka ci abinci a ciki yana da muhimmanci sosai, ya zama wata irin al'adu. Dakin cin abinci na Tiandiyijia da ke kusa da titin Nanchizi aka samu shi ne bayan da aka yi kwaskwarima kan wani gidan kwana mai fasali hudu irin na gargajiya na Beijing. A da watakila dattijai sun taba zama a wannan gidan kwana mai fasali hudu irin na gargajiya na Beijing, shi ya akwai abubuwan tarihi da yawa a ciki, haka kuma, zane-zanen da ke kan bango sun nuna halayen musamman irin na kasar Sin.'

Mai yiwuwa ne mutanen da suka zo kasar Sin ziyara a karo na farko daga kasashen waje za su gamu da matsala, wato ko cin abinci a dakin cin abinci na Quanjude domin kara saninsu kan al'adun kasar Sin mai dogon tarihi, ko kuma cin abinci a dakin cin abinci da ake gasa agwagi ta sabbin hanyoyi domin kara fahimta kan kasar Sin na zamani. Amma duk da haka, masu sauraro, in kun kawo wa kasar Sin ziyara a wannan lokacin zafi, to, tabbas ne za ku ci wannan shahararren abinci wato gasassun agwagi irin na Beijing.(Tasallah)


1 2 3