Ko a kasar Sin ko kuma a kasashen ketare, gasassun agwagi irin na Beijing sun riga sun shahara sosai, har ma mutane da yawa in sun tabo magana kan abincin kasar Sin mai dadin ci, to, nan da nan su kan tuna da gasassun agwagi irin na Beijing. To, mane ne halin musamman na irin wannan abinci? A ina ne za a iya cin irin wannan agwagi mai dadin ci? A cikin shirinmu na yau, bari mu zagaya Beijing tare da wakilinmu domin kara saninmu kan gasassun agwagi irin na Beijing.
Wang Rong shekarunsa ya kai 54 da haihuwa, ya riga ya yi shekaru 30 ko fiye yana gasa agwagi a dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi mai suna Quanjude na Beijing. Wannan babban kuku na reshen dakin cin abinci na Quanjude a Hepingmen ya bayyana cewa, yau ya rage kwanaki kadan a bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, yana matukar fatan baki da suka zo kasar Sin domin kallon gasar wasannin Olympics za su dandana gasassun agwagi da suke samarwa. Ya ce,'Gasasshiyar agwagwa na daya daga cikin abinci da suka fi shahara a kasar Sin. Sinawa su kan ce, in ba ka ziyarci babbar ganuwa ta kasar Sin ba, to, za ka yi da-na-sani, haka kuma, tabbas ne za ka yi da-na-sani, in ba ka ci gasasshiyar agwagwa ba. In ka zo kasar Sin, ka yi ziyara a Beijing, musamman ma a lokacin gasar wasannin Olympics, tabbas ne ka kalli gasanni da kai ziyara ga babbar ganuwa ta kasar Sin da kuma ci gasassun agwagi.'
Dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi mai suna Quanjude ya yi shekaru fiye da 140 yana sayar da gasassun agwagi. Reshensa na Hepingmen a cibiyar Beijing an kafa shi a shekarar 1979, shi ne dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi mafi girma a duk duniya. A ko wace ran ya kan maraba da baki daga gida da kuma waje sama da dubu 3.
A matsayin dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi mai dogon tarihi, sunan Quanjude na kusan kasancewa alamar musamman da ke wakiltar gasassun agwagi irin na Beijing. Game da halayen musamman na gasassun agwagi da ake samarwa a dakin cin abinci na Quanjude, kullum Mr. Wang ya ji alfahari sosai, ya ce,'In bakinmu sun ga wata gasasshiyar agwagwa mai kiba da yawa da muke samar musu a tebur, su kan rasa abin da za su yi, kukunmu su kan yanke naman agwagwar tamkar yadda warkokin nama ke nan. In wani ya nuna sha'awa sosai, to, ya iya yanke naman agwagwa da kansa, ta haka, zai kara jin farin ciki bisa cin naman da ya yanke.'
1 2 3
|