Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 15:43:26    
Ziyarar da jarumin wasannin Olympic ya kawo wa kasar Sin

cri

A watan Yuni na shekarar 2008, a matsayin mai sauraronmu da ya ci gasar kacici-kacici ta gasar wasannin Olympics ta Beijing, Mr. Akhwari ya sake zuwa kasar Sin! Bayan rabin shekara, mun sake saduwa da wannan jarumin wasannin Olympics, wanda tsawon shekaru ba su canza surarsa sosai ba. Da zarar mu sadu da shi, mun gane fara'ar jama'ar Afirka, kuma mun gane kaunarsa kan Beijing. Ya yi zumudi sosai, ko da yake bai iya Sinanci sosai ba, amma ya gaya mana cikin Sinanci cewa,'Sannu, Beijing! Na iso!'

Mr. Akhwari ya sha gamuwa da matsaloli a kan hanyarsa ta zuwa Beijing. Ya tashi daga garinsa cikin mota domin zuwa gunduma, daga baya ya je birnin Arusha, inda ya shiga jirgin kasa zuwa birnin Dar Es Salaam, hedkwatar kasar Tanzania, a karshe dai ya isa birnin Doha, hedkwatar kasar Qatar cikin jirgin sama, inda ya sake shiga jirgin sama daban domin zuwa Beijing. Wannan ya ba wannan tsoho mai shekaru kusan 70 da haihuwa wahala sosai. Amma Mr. Akhwari ya gaya mana cewa, a lokacin da ya sake numfashin iskar Beijing, ya fahimaci karin yanayin wasannin Olympics, bai ji gajiya ba. Wasannin Olympics su kan faranta ransa sosai, ya kuma yi abun dariya da cewa, watakila an haife ni ne domin wasannin Olympics, shi ya sa a duk ransa yana raka wasannin Olympics.

Mr. Akhwari ya burgi dukkan mutanen da suka gan shi a filin jirgin sama. A cikin shekaru 40 da suka wuce, ruhun Mr. Akhwari na rasa daina yin abun da ya sa gaba ya karfafa gwiwar mutanen da ba a iya kidaya yawansu ba. Tabbas ne ziyararsa a Beijing za ta karfafa gwiwar mutanen Sin da yawa da su ci gaba da ba da gudummowa wajen shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008. Mutane sun kasa daurewa sai dai suka yi ihu cewar, jarumin ya zo!(Tasallah)


1 2 3