Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 15:43:26    
Ziyarar da jarumin wasannin Olympic ya kawo wa kasar Sin

cri

A gun gasar wasannin Olympics ta birnin Mexico ta shekarar 1968, magujin gudu na dogon zango John Stephen Akhwari na kasar Tanzania ya kammala gasar gudun Marathon tare da jin rauni a kafarsa. Ya yi mana bayani kan ruhun wasannin Olympics bisa karfin zuciyarsa. Bayan shekaru 40, wato a jajibirin gasar wasannin Olympics ta Beijing, a matsayinsa na bako da gidan rediyonmu ya gayyata, wannan jarumi wato Mr. Akhwari ya kawo wa kasar Sin ziyara. A cikin nan da kwanaki 3 masu zuwa, za mu yi cikakken bayani kan ziyarar da wannan jarumin wasannin Olympics ya kawo wa kasar Sin. Yau ma za mu gabatar muku da bayanin musamman na farko.

Kullum ba a rasa jarumai a gun gasannin wasannin Olympics na zamani da aka yi a cikin shekaru 100 ko fiye da suka wuce ba, haka kuma, ba a rasa tafi da aka yi ba a gun gasannin wasannin Olympic.

Amma a cikin shirin gudun Marathon na gasar wasannin Olympics ta birnin Mexico da aka shirya yau da shekaru 40 da suka wuce, an yi ban tafi ga wani maguji kawai, wato magujin gudu na dogon zango John Stephen Akhwari na kasar Tanzania. Shi ne wanda ko da yake ya ji rauni a kafarsa, amma ya jure ciwo mai tsanani, ya kammala hanyar Marathon mai tsawon kilomita 42.195 a kan tudun da ke birnin Mexico.

Saboda kusantowar gasar wasannin Olympics ta Beijing, wannan jarumin wasannin Olympics ya kara shahara a kasar Sin. Gao Jiatong, wata karamar yarinya daga wani nasare a Beijing, shekarunta ya kai 4 kawai da haihuwa. A yayin da wakilinmu ya tambayi yaran da ke wannan nasare ko sun san wani jarumi mai suna John Akhwari ko a'a, wannan yarinya ta dauki jagoranci wajen ba da amsarta. Ta ce,'Na san dattijo Akhwari. Ko da yake ya ji rauni, amma ya ci gaba da gudu. Dukkanmu muna sonsa. Na kan zo nasare tare da hotonsa. Ya kamata mu yara mu yi koyi da shi, bai ji tsoron ciwo ba, ya ci gaba da gudu.'


1 2 3