Watakila a idon kananan yara, wannan jarumi tsoho shi ne sabon aboki a gare su. Amma a zukatan Sinawa tsofaffi masu yawa, Mr. Akhwari abin koyi ne a gare su da ya karfafa gwiwarsu. Ge Xiaoxia, wata mazauna Beijing, ta riga ta yi ritaya daga aiki. Game da Mr. Akhwari, madam Ge ta gaya mana cewa,'Labarin Akhwari ya burge mu sosai. Ina tsammani cewa, ko da yake ba mu kalli gasarsa kai tsaye ba, amma a zukatanmu, mun yi masa tafi a tsaye. Mun fi girmama ruhunsa, wanda shi ne ainihin ruhun wasannin Olympics, wato rasa jin tsoron yin gwagwarmaya da kuma daina abun da aka yi, yin iyakacin kokari domin samun maki mai kyau. Shi ya sa tilas ne mu yi koyi da shi, bai kamata mu ji tsoron tsufa ba, mu rike da wannan ruhu.'
Ba fararen hula na kasar Sin kawai ba, ruhun wannan jarumin wasannin Olympics ya burge dimbin mashahurra na kasar Sin. You Hongming, wani shahararren mawaki na kasar Sin shi ma ya mai da hankali kan wannan jarumi.
Mr. You ya rubuta ta domin Mr. Akhwari ba tare da yin barci har kwanaki 3 ba. Dangane da dalilin da ya sa ya rubuta wannan waka mai suna 'Jarumi', Mr. You ya ce,'A ganina, ruhunsa na yin gwagwarmaya ya burge ni sosai. Nan da nan ina alla-alla wajen rubuta masa wata waka. Mutane da yawa sun fito da wakoki da yawa kan wasannin Olympics. Amma yawancin wakokin sun karfafa gwiwar 'yan wasa da su nemi zama zakara. Duk da haka, ina tsammani cewa, babu wanda ya rubuta wata waka kan wanda ko da yake ya jikkata, amma ya nemi kammala gasa a madadin kasarsa. Shi ya sa na tanadi wannan ruhu da wannan labari cikin wakar.'
Fito da bidiyon wake-wake na waka mai suna 'Jarumi' ya zama wata dama ga Mr. Akhwari da ya kawo wa kasar Sin ziyara a karo na farko a watan Disamba na shekarar bara. Game da abubuwan da suka faru a lokacin da suke rera waka mai suna 'Jarumi' tare, Mr. You ya ce, wannan tsoho ya yi kuka saboda ganin surarsa a lokacin can a cikin wannan bidiyo, kuma yana kishin wannan waka sosai. Mr. You ya gaya wa wakilinmu cewa,'Ba ni da nufin neman koya masa da gangan, amma ya iya rera wakar kadan. An fasara masa jimlolin wakar daya bayan daya. Yana saurara yana gwada. Ya san wakar ta bayyana ruhunsa na yin kokari ba tare da kasala ba. Yana ganin cewa, wannan waka na da dadin ji.'
A cikin bidiyon wake-wake da aka dauka kan wannan waka, Wang Huiyue, wani dan wasan kwaikwayo ya zama mutumin da ya gaji ruhun Mr. Akhwari. Wannan saurayi mai kyan gani ya yi hira da wakilinmu kan abubuwan da suka faru a lokacin da yake tuntubar Mr. Akhwari a lokacin daukar bidiyon. Ya ce,'Ina girmama shi kwarai da gaske. Da zarar na yi musafaha da shi, na ji karfinsa. A lokacin daukar bidiyon, a duk yamma, na yi aiki tare da shi. Na gane kaunarsa kan wannan hanyar gudu bisa abubuwan da ya nuna a idonsa, ya kuma taba hanyar gudun.'
A karo na farko da Mr. Akhwari ya zo kasar Sin, Wang Huiyue ya ba shi wata kwaryar da aka yi da tagulla kamar abun kyauta, yana fatan Mr. Akhwari ya iya gano girmamawa da ake nuna masa, kuma ruhunsa ya karfafa gwiwar mutanen Sin da yawa. Da jin labari na wannan tsoho ya sake zuwa Beijing, wannan saurayi ya yi farin ciki sosai, ya ce,'Ina son shi da ni mu za mu sake kallon bidiyon wake-wake da muka yi tare. Ina matukar fatan zan iya sadu da shi, kuma karin mutane za su ga shi, za su nuna masa girmamawa.'
1 2 3
|