
Jar kasa da ke cikin filin wasan kwallo na zamani na softball na da muhimmanci sosai. Saboda 'yan wasa da kan zame a cikin gasar wasanni, shi ya sa kada jar kasa ta yi yauki sosai, kada kuwa ta yi tauri sosai, ta kasance cike da rabin rairayi. Don haka, an kashe kudin Sin yuan miliyan 2 domin sayen jar kasa daga kudancin kasar Sin, an shimfida shi a filayen horo na filin wasan kwallo na zamani na softball na Fengtai. Jar kasa da ke cikin babban filin wasa da filayen wasan na ko-ta-kwana ne aka sayo daga ketare.
Ko da yake an kashe dimbin kudi wajen sayen jar kasa, amma an yi tsimin kudi a fannoni da yawa a wannan filin wasa. Ana amfani da fitilu da kayayyakin wanka irin na tsimin makamashi a wannan filin wasa, sa'an nan kuma, ana amfani da hasken rana wajen samar da ruwa mai zafi a filin wasan, ta haka an yi tsimin dimbin makamashi.
Dadin dadawa kuma, filayen ciyayi da aka shimfida a wannan filin wasa na iya shan ruwan sama cikin sauri, ta haka, bayan awa daya da aka dauke ruwa, za a iya yin gasa. Ta hanyar bututun da ke karkashin filayen ciyayi ne aka tattara ruwan sama, an iya sake amfani da ruwa. 1 2 3
|