Cibiyar tseren kwale-kwale ta wasannin Olympics ta Qingdao ta gudanar da dukkan wadannan abubuwa ne domin ba da kyakkyawar hidima ga 'yan wasa masu shiga tseren. Bisa labarin da wakilinmu ya samu, an ce, ya zuwa yanzu, kungiyoyin 'yan wasan kwale-kwale na kasashe da shiyyoyi 44 sun riga sun isa birnin Qingdao don yin horaswa. A hakika dai, yau da shekaru 2 ko 3 da suka gabata, wasu kasashen da ke nuna gwaninta a fannin tseren kwale-kwale ciki har da kasar Italiya sun riga sun aika da mutane zuwa birnin Qingdao don samun labarai. Qu Chun, mataimakin babban sakatare mai kula da ayyakan tsere na kwamitin ya gaya mana cewa,
"A shekara ta 2005, kasashen Italiya da Faransa da Amurka da kuma Birtaniya sun riga sun zo birnin Qingdao don yin bicike kan wurin yin tseren kwale-kwale, suna mai da hankali sosai kan fahimtar wurin yin tsere. Ban da wannan kuma dimbin ma'aikata masu kula da ayyukan ba da hidima na kasashen sun zo birnin tun tuni domin fahimtar wayar salula da abinci da dakunan kwana da kuma wurin tsere, ta haka muna iya gano cewa, lalle wannan wani kyakkyawan tsari ne na ba da tababci."(Kande Gao) 1 2 3
|