Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 15:33:38    
Cibiyar tseren kwale-kwale ta wasannin Olympics ta birnin Qingdao

cri

A hankali a hankali, igiyar ruwan teku tana ta bugun gefen teku na cibiyar tseren kwale-kwale ta wasannin Olympics ta birnin Qingdao, inda jama'a za su iya kallon tseren a lokacin da ake yin tseren kwale-kwale na wasannin Olympics na Beijing. Kwamitin shirya tseren kwale-kwale na wasannin Olympics na birnin Qingdao ya karya ka'idojin da aka saba bi a cikin wasannin Olympics na da, wato 'yan kallo suna iya kallon tseren kwale-kwale a kan jiragen ruwa kawai, yanzu muddin an biya kudin Sin wato Yuan 20, to za a iya kallon tseren a gefen teku. Pang Liang, wani mutum mai aikin sa kai na tseren kwale-kwale na wasannin Olympics da ya samu iznin gudanar da aikin ba da jimawa ba ya bayyana cewa,

"Akwai tikiti iri biyu na wannan tseren kwale-kwale. Daya shi ne tikitin jirgin ruwa, wanda ake bukatar sayensu a kan Internet. Dayan shi ne tikitin kallon tseren, farashinsa ya kai Yuan 20 kawai, amma ba za a iya sayensa kafin ranar yin tseren ba, shi ya sa mazaunan birnin Qingdao da kuma masu yawon shakatawa dukkansu suna iya kallon tseren tsakanin kwale-kwale fiye da dubu a kusa."


1 2 3