Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 15:33:38    
Cibiyar tseren kwale-kwale ta wasannin Olympics ta birnin Qingdao

cri

Domin share fage ga tseren kwale-kwale na wasannin Olympics da kuma na nakasassu, dukkan ma'aikatan kwamitin shirya tsaren na birnin Qingdao suna yin iyakacin kokari domin gudanar da ayyuka mafi kyau. Su Wenjie, shugaban sashen gudanar da ayyukan watsa labarai na kwamitin ya gaya mana cewa, an riga an kammala dukkan ayyukan share fage, yanzu suna tsara wasu shirye-shirye na filla filla. Kuma ya kara da cewa,

"Game da dukkan ayyukan share fage ga tsaren kwale-kwale na wasannin Olympics, a shirye muke, abin da muke yi yanzu shi ne tsara shirye-shirye na filla-filla kan ayyuka iri daban daban. Mun riga mun shirya dukkan kayayyakin gida da ruwa da wutar lantarki da kuma sauran kayayyaki da ke cikin dakunan wasanni, yanzu muna jarraba su a tsakane. Ban da wannan kuma, dukkan kayayyakin da za a bukata wajen yin tseren da kuma kwale-kwale a shirye suke, yanzu muna jarraba su domin tabbatar da gwanin babu matsala. Bugu da kari kuma za mu ci gaba da gudanar da ayyukan ba da hidima ga kungiyoyin 'yan wasa na kasashe daban daban."


1 2 3