Ban da aikin nuna hanyoyi ga mutane, Gao Yuhong ta tura membobin kungiyarta zuwa kungiyar agaji ta RedCross, domin karbar horon musamman kan bayar da gudummowa cikin gaggawa, da makarantar kurame domin koyon alamun magana na yau da kullum da kurame suke yi da hannayensu, a wani yunkurin taimakawa masu yawon shakatawa wajen haye wahalhalu. "Alal misali, wata rana, wata karamar yarinya ta suma ba zato ba tsammani a kofar Fadar Bazara wato Yiheyuan. Ba tare da bata lokaci ba, na je wurin domin duba halin da take ciki. Mun taba karo ilimi kan yadda za mu yi domin tinkarar irin wannan lamarin ba-zata daga wajen kungiyar agaji ta RedCross. Shi ya sa nan da nan ne na buga lambar 120, sa'annan wata motar asibiti ta zo."
Domin bayar da hidima ga gasar wasannin Olympics ta Beijing da kyau, membobin kungiyar nuna hanyoyi wadanda suka ji tsoron yin magana cikin harshen Turanci a lokacin da, sun gayyaci wani malami domin koyar musu da Turanci. Bayan da suka samu wannan horo, a halin yanzu, suna iya magana cikin harshen Turanci. Yayin da wakilinmu ke hira tare da Madam Gao, tana magana da wasu jumloli cikin Turanci. Ta ce: "How can I get to the Lama Temple? Wato yaya zan je haikalin Lama? Tian'anmen Square, wato filin Tian'anmen ke nan. Na fahimci dukkansu. Daga baya sai na amsa cewa, 'from here cross the street, you will find the bus stop behind with it, please take the bus number 690 to Tian'anmen Square''.
Yayin da take hira da wakilin gidan rediyonmu, Gao Yuhong, 'yar shekaru 45 da haihuwa, tana sa ran alheri ga gasar wasannin Olympics ta Beijing wadda za'a shirya nan ba da jimawa ba. Ta ce: "Tare da karatowar gasar wasannin Olympics ta Beijing, akwai karin masu yawon shakatawa wadanda za su zo nan kasar Sin ziyara. Ya kamata mu kokarta ba tare da kasala ba wajen bayar da kyakkyawar hidima ga baki 'yan kasashen waje, domin nuna kyakkyawar halayyar Sinawa da ta Sinawa masu aikin sa-kai."
A matsayin muhimman membobi na babban iyalin mutane masu aikin sa-kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing, ba ma kawai masu aikin sa-kai na birnin sun yi bayanai kan hanyoyi daban-daban ga masu yawon shakatawa na gida da na ketare ba, hatta ma ya kamata su yada kyakkyawar halayyar masu aikin sa-kai, da fadada ilimomi kan gasar wasannin Olympics. A halin yanzu, sun riga sun shirya sosai wajen bayar da gudummowarsu ga gasar wasannin Olympics ta Beijing. 1 2 3
|