Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-24 19:29:54    
Masu aikin sa-kai na birni na gasar wasannin Olympics ta Beijing suna tafiyar da ayyukansu ba ji ba gani

cri

Bisa shawarwarin da Madam Gao ta bayar, domin kyautata aikin bada hidima ga masu yawon shakatawa a Fadar Bazara wato Yiheyuan, a watan Agusta na shekarar 2006, ofishin titin Qinglongqiao na gundumar Haidian ta birnin Beijing ya kafa wata tashar nuna hanyoyi ga masu yawon shakatawa a kofar Fadar Bazara. Wannan karamar kungiya na kunshe da masu aikin sa-kai guda 14, wadanda su kan je kofar Fadar Bazara a kowane karshen mako domin bayar da hidima ga masu yawon shakatawa.

"Da farko, akwai mutane sama da 10 wadanda suka shiga wannan aiki. Sannu a hankali ne, yawan mutane masu aikin sa-kai a kungiyarmu na kara karuwa, ciki har da mazauna birni, da daliban jami'o'i daban-daban, da masu aikin kwana-kwana na Fadar Bazara. A halin yanzu, adadinsu ya riga ya tasam ma dari guda."

A matsayin wani shahararren wurin yawon shakatawa a nan birnin Beijing, yawan masu yawon shakatawa da Fadar Bazara ta karba a kowace rana ya zarce dubu dari. A kowace tashar motar safa a kofofi daban-daban na Fadar Bazara, muna iya ganin masu aikin sa-kai na wannan karamar kungiyar nuna hanyoyi ta gundumar Haidian wadanda suke aiki tukuru wajen taimakon masu yawon shakatawa. Bisa labarin da muka samu, an ce, tun daga watan Agusta na shekarar bara, membobin wannan karamar kungiya sun riga sun bayar da taimako ga masu yawon shakatawa na gida da na ketare ba tare da samun kudi ba da adadinsu ya zarce dubu 60. Tare da karatowar gasar wasannin Olympics ta Beijing, membobin kungiyar nuna hanyoyi ta gundumar Haidian sun shiga aikin sa-kai na birni na gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Gao Yuhong ta kan nuna tsauraran matakai a kan membobin kungiyarta. Ta bukaci membobin kungiyar da su yi aiki a tsanake, kada su ce "Ban sani ba". "Na bukaci membobin kungiyarmu da kada su ce 'Ban sani ba' yayin da suke aiki. Idan mun gamu da wata matsalar da ba mu iya warware ba, to, za mu gaya mai yawon shakatawa cewar: Ko za ka iya gaya mana lambar wayar tarho taka, da zarar mu samu amsa, za mu buga maka waya ba tare da bata lokaci ba."

A ganin Gao Yuhong, aikin nuna hanyoyi ga mutane, ba ma kawai a gaya musu wace motar safa za su dauka ba, hatta ma a san ina ne za ka iya yin hayar keken guragu, ina ne za ka iya sayen magunguna, ina ne za ka iya samun kudi, ina ne za ka iya daukar hoto cikin gaggawa. Ko da yake ba ta iya tafiya yadda ya kamata ba, amma ta yi iyakacin kokari wajen gudanar da aikinta. Wani lokaci, domin gayawa masu yawon shakatawa daga wuri kaza zuwa wuri kaza ya kai mita kaza, ta kan je wannan wuri da karfin kanta bisa taimakon sandunan guragu biyu.

1 2 3